A ranar Lahadi tawagar kwallon kafa ta Sifaniya ta tashi wasa 2-2 a gidan Jamhuriyar Czech a wasa na bibiyu a Nations League kuma minti hudu da fara wasa mai masaukin baki, ta ci kwallo ta hannun Jakub Pesek, kwallo mafi sauri da aka zura a ragar Sifaniya a wasa 39 da Luis Enrikue ke jan ragama.
Daga baya Pablo Gabi ya farke a minti na 45, ya zama matashin da ya ci wa tawagar Sifaniya kwallo mai karancin shekarun haihuwa mai shekara 17 da kwana 304 kuma a baya wanda ya ke da tarihin a baya shi ne Ansu Fati, wanda ya ci Ukraine, yana da shekara 17 da kwana 311.
Jan Kuchta ne ya ci wa Jamhuriyar Czech kwallo na biyu, sai dai dab da za a tashi Sifaniya ta farke ta hannun Inigo Martinez. Sifaniya ta fara tashi 1-1 da Portugal a gida ranar Alhamis biyu ga watan Yuni, za kuma ta karbi bakuncin Jamhuriyar Czech ranar Alhamis 9 ga watan Yuni a dai gasar ta Nations League.