A jiya Lahadi ne zaunannun mambobin ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS karo na 20, suka gana da ’yan jaridu na kasar Sin da na kasashen ketare.
A yayin taron, babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping ya ba da jawabi, inda ya ce a halin yanzu, kasar Sin tana kan tafiyar da aka sanya a gaba, domin gina wata kasa mai tsarin gurguzu bisa dukkan fannoni cikin wannan sabon zamani, tana kuma dukufa domin cimma burinta a lokacin cika shekaru 100 da kafuwar Jamhuriyyar Jama’ar Kasar Sin, wato zuwa tsakiyar karnin nan, kuma kasar Sin za ta gina wata kasa mai karfi bisa tsarin gurguzu cikin wannan sabon zamani, wato wata kasa mai matsakacin wadata, da dimokuradiyya, da wayewar kai, da zaman daidaito, kuma mai kyau, ta yadda za ta tabbatar da farfadowar kasa baki daya, bisa salon ci gaba iri na kasar Sin cikin sabon zamani.
Haka kuma, cikin jawabinsa, Xi ya bayyana babban aikin JKS, inda ya jaddada cewa, ya kamata a ci gaba da taimakawa jama’ar kasar wajen cimma burinsu na kyautata zaman rayuwa, yayin da ake gina wata kasa mai matsakacin wadata, wadda za ta kara samar da damammaki ga duniya baki daya.
Kaza lika, bayanin da ya yi game da “salon ci gaba iri na kasar Sin cikin sabon zamani” ya janyo hankulan masu sa ido na kasashen duniya.
A yayin babban taron wakilan JKS karo na 20, an ba da shawara kan yadda za a gina wata kasa mai tsarin gurguzu bisa dukkan fannoni cikin wannan sabon zamani, da kuma yadda za a inganta farfadowar kasar baki daya.
Idan aka kwatanta da salon ci gaba iri na yammacin kasashen duniya, wanda ya fi mai da hankali kan kudi, da kwashe albarkatun sauran kasashe, za a gane cewa, salon ci gaba iri na kasar Sin ya warware matsaloli da dama dake kan hanyar neman ci gaban bil Adama, da kuma samar da wata sabuwar hanyar neman ci gaba cikin sabon zamani ga dukkanin bil Adama.
Haka kuma, Xi Jinping ya jaddada cewa, za mu yi aiki da sauran al’ummomin kasashen duniya, domin ci gaba da gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil Adama, kuma, kasar Sin za ta kara bude kofa ga waje, domin samar da karin damammaki ga duniya.
Bugu da kari, sakamakon da aka cimma a yayin taron wakilan JKS karo na 20, da sanawar da shugaban kolin kasar Sin ya yi, sun kara fahimtar da jama’ar kasashen duniya kan wani muhimmin batu, wato, Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, jam’iyya ce mai muhimmanci wajen tabbatar da gudanarwar harkokin kasa yadda ya kamata, kuma, muhimmiyar jam’iyya ce, wadda za ta tabbatar da ginawar wata kasa mai tsarin gurguzu bisa dukkan fannoni a sabon zamani, da kuma inganta farfadowar kasa bai daya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)