Allah ya yi rasuwa wa tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Bello Musa Kofarmata.
Ya rasu ne a daren ranar Talata yana da shekara 34 a duniya bayan wata yar gajeruwar rashin lafiya da ta sameshi a gidansa da ke unguwar Kofarmata a jihar Kano.
Tsohon mataimakin shugaban kungiyar marubuta labarin wasanni na shiyyar Arewa Maso Yamma, Ado Salifu shi ne ya tabbatar wa LEADERSHIP rasuwar, ya ce, tunin aka yi jana’izar mamacin da safiyar ranar Laraba kamar yadda addinin musulunci ya tanadar a Kofarmata da ke Kano.
Kofarmata dai ya shiga kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ce a shekarar 2007 ya kuma taimaka wa kungiyar wajen samun nasara a yayin gasar Premier league ta Nijeriya da aka gudanar 2007/2008 da kwallaye 11. Kuma shi ne wanda ya fi zura kwallaye da suka kai su ga nasara.
Ya bar kungiyar Kano Pillars a shekarar 2010 inda ya shiga kungiyar kwallon kafa ta Heartland FC da ke Owerri daga baya ya sake barinta a shekarar 2012 kuma ya shiga kungiyar Elkanemi Warriors da ke Maiduguri.
Ya sake komawa tsohowar kungiyarsa kafin daga bisani ya fita daga kasar Nijeriya tare da sanya hannun kwantiragi da kungiyar IK Start of Norway.
Marigayi Kofarmata ya kasance cikin ‘yan wasannin Nijeriya (Maza) ‘U20’ da suka taka leda, Flying Eagles squad zuwa Canada 2007 FIFA U20 World Cup.
Ya buga wa manyan ‘yan wasan Nijeriya Super Eagles wasa guda daya, a wasan sada zumunci da suka yi da Jamhuriyar demokraxiyya Congo da suka samu ci 5-2 a Abuja a watan Maris na 2010 da sauran wasanni da dama da ya nuna bajintarsa a ciki.