Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annuti (EFCC) sun kai wani samame a ranar Talatar da ta gabata a haramtacciyar kasuwar ‘yan canji da ke Wuse Zone 4, Abuja, inda suka cafke wasu masu gudanar da kasuwar da ke da ofisoshin a yankin.
Daya daga cikin ‘yan kasuwar, wanda ya bayyana sunansa da Sani, ya shaida wa Jaridar Daily Trust cewa jami’an sun zo ne a cikin motoci uku sannan suka ajiye su a wurare daban-daban.
Ya ce an kama wasu abokan aikinsa.
Alhaji A. Mohammed, wani daga cikin masu gudanar da kasuwar, ya ce jami’an tsaro sun yi samame a kwanan baya a kasuwar inda suka cafke wasu daga cikin ‘yan kasuwar.
A makon da ya gabata ne babban bankin Nijeriya ya sanar da shirin sake fasalin wasu kudade domin dakile hauhawar farashin kayayyaki, tun daga wannan lokaci jami’an EFCC da sauran jami’an tsaro suka baza komar su a kasuwar.
Da aka tuntubi Kakakin Hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar wa Daily Trust da kai samamen, amma bai yi wani karin haske game da hakan ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp