Akalla ‘yan bindiga takwas ne da ‘yan banga shida suka mutu a wata musayar wuta tsakanin kungiyoyin biyu a kewayen Kundu, kusa da Zungeru a karamar hukumar Wushishi ta Jihar Neja.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 9 na daren ranar Talata, inda aka kuma yi awon gaba da wasu mutane.
- Kasar Sin Za Ta Kara Samar Da Wutar Lantarki Ta Amfani Da Makamashin Nukiliya
- Babu Barazanar Kai Hari A Kano – ‘Yansanda
Leadership Hausa ta samu labarin cewa al’ummar yankin sun samu bayanai kan yadda ‘yan bindigar suka sace garken shanu masu yawa suka fito daga Kundu zuwa kauyen Akere inda suka kammala shirin kai musu hari.
Sai dai a cewar wata majiya, ‘yan bindigar sun samu nasarar shirin ne ta hanyar masu kai musu rahoto a cikin al’umma inda daga bisani suka fara kai farmaki kan ‘yan banga wanda ya kai ga yin luguden wuta.
“An kididdiga abubuwan da suka faru a bangarorin biyu. Mutane da yawa sun samu raunuka daban-daban daga bangarorin biyu, yayin da wasu mazauna unguwarmu aka yi garkuwa da su zuwa wani wuri da ba a san ko ina bane,” in ji majiyar.
An kuma rawaito cewa sojojin da ke sansanin Zungeru sun tallafa wa ‘yan banga wajen yakar ‘yan bindigar.
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun ta ci tura a lokacin da ake hada wannan rahoto.