Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa (NCS) a Jihar Kebbi, ta kama wasu kayayyakin fasa kwauri da kudinsu ya kai Naira miliyan 78.6 a watan Oktoban 2022 a jihar.
Shugaban hukumar Kwastam, Mista Joseph Attah ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a kan ayyukan hukumar na watan Oktoba a Birnin Kebbi.
- Shugaba Xi Zai Gabatar Da Jawabi A Yayin Bude Baje Kolin CIIE Karo Na 5
- Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Samar Da Fa’ida A Zahiri Ga Jama’ar Afirka
Ya ce rundunar ta samu nasarori a cikin muhimman ayyukan da suka shafi aikin dakile fasa kwauri, ta samar da kudaden shiga da kuma saukaka kasuwanci.
A cewarsa: “An ci gaba da samun karuwar kudaden shiga na hukumar. A tsawon lokacin da ake bitar, mun samar da zunzurutun kudi har Naira miliyan 162.2 a matsayin kudaden shiga daga harajin shigo da kayayyaki. Wannan shi ne mafi girma tun bayan bude iyakar ta Kamba da ke a Jihar ta Kebbi.
“Rundunar ta kuma taimaka wajen fitar da kayayyakin da ake sarrafa su a cikin gida na sama da Naira biliyan 2 a daidai lokacin da ake gudanar da bincike,” in ji Attah.
Ya ce, rundunar ta umurci jami’ansu da su kara sanya ido a cikin lungu da sako na lungu da sako na ruwa a kokarinsu na dakile ayyukan fasa-kwauri a cikin lungu da sako na jihar.
“Saboda haka, kokarin da aka yi ya haifar da kama wasu kayayyaki iri-iri har 16 da suka hada da, fakiti 284 na kwamfutar tafi-da-gidanka, tabar wi-wi, motoci 4 da aka yi amfani da su, wadanda kuma akwai Motocin na shi ga jama’a kirar Honda guda biyu da aka yi amfani da su, da motar dizal guda daya da kuma babbar motar tifa.
“Sauran sun hada da, bale 139 na tufafin hannu, buhunan shinkafa 345 na kasar waje (kowanne kilogiram 50), lita 2,250 na man fetur (PMS), kwali 38 na man shafawa (bleaching cream), guda 80 na batura masu amfani da hasken rana, da dai sauransu.
“Abin da ake tsamani da za a biya na harajin kayayyakin da aka kama ya kai Naira miliyan 78.6,” inji shi.
Kazalika, Mista Attah ya bayyana kudurin rundunar na tabbatar da cewa wadanda suka zabi shigo da kaya ko fitar da su ta iyakar Kamba, sai bin ka’idojin da suka dace na dokar kasa.
“Za ku yarda da ni, cewa yayin da sauran kayayyakin da aka kama na da kididdigar kudi, ba za mu iya kididdige yawan barnar da kwayoyi masu hadari da sauran abubuwa ke haifarwa a cikin al’umma ba.”
Bugu da kari ya ce “Irin wannan abu idan aka fito da shi a cikin al’umma yana taimaka wa dukkan manyan laifukan da muke gani a cikin al’ummarmu.
“Za a mika tabar wi-wi ga hukumar NDLEA jihar Kebbi domin daukar matakin da ya dace,” in ji shi.
Daga karshe dai, mista Joseph Attah ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da aikin da aka ba su na dakile ayyukan fasa kwaurin ba tare da kasawa ba duk da kalubalen da ake fuskanta daga ‘yan kasa masu taimaka wa ga aikata miyagun laifuka a kan jami’ansu.