Kimanin manoman alkama 200 ne wadanda suka fito daga sassa daban-daban na Jihar Jigawa za su amfana da shirin NALDA a noman rani na wannan shekara ta 2022.
Jagoran NALDA a Jihar Jigawa, Malam Bello Umar ne ya bayyana haka a yayin taron wayar da kan manoma a kan shirin na NALDA wadda ya gudana ranar Litinin da ta gabata a garin Kazaure.
- Yadda BBC Hausa Ya Karrama Gwarazan Gasar Waƙa Da Hikayata Ta Bana
- Sin Ta Sanar Da Shirin Bunkasa Fasahar VR
Malam Umar ya ce duba da yadda Allah ya albarkaci jihar da kasar noma ya sa NALDA ta zabi garin Marke karkashin karamar hukumar Kaugama a shekarar da ta gabata da kuma yankin Gumuna-Gora a Kazaure a noman rani na wannan shekara ta 2022.
Jagoran wadda ya ce tuni shirye-shirye sun yi nisa, ya ce tuni manoman sun fara gyare-gyaren gonakinsu da kaftu domin fara aikin alkamar wadda nan ba da dadewa ba za a raba musu sauran kayayyakin.
Ya karawa cewa kayayyakin sun hada da magunguna da injin feshi da ingantaccen iri da takin zamani da injin ban ruwa da injin girbin amfanin gona tare da ba su tabbacin ingantaccen farashi idan Allah ya yi amfanin.
“A shekarar 2020, an yi wa wannan shiri lakabi da taken ‘A dama da kowa’ wadda ya mayar da hankali wajen magance barazanar yunwa a duniya baki daya.
“Duba da har zuwa yanzu akwai barazanar karancin abinci sakamakon kalubalan annoba da kuma canjin yanayi ya sa taken shirin a wannan shekarar ya maida hankali wajen kira ga kungiyoyin manoma da sauran manyan manoma su yi amfani da sabbin dabarun noma na zamani domin cimma nasarar samar da wadataccen abinci saboda magance yunwa a duniya baki daya.
A yayin taron bitar an gabatar da mukaloli da suka shafi noman alkama tare da kara wa juna sani tsakanin manoma matasa da mata Manoma.