Wata mata mai suna Cecilia Idowu, mai kimanin shekara 55, ta gurfana a gaban wata babbar kotun majistare da ke Akure, ta jihar Ondo bisa zargin kashe danhayar da ke gidanta.
Mai gabatar da kara ya ce, wadda aka gurfanar ta kashe ta kashe wani mai suna Stephen Haruna, a gidanta da ke Oke-Igbalao, Akoko a karamar hukumar Arewa maso yamma da ke jihar.
- Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin PDP A Kaduna Ta Tsakiya, Ta Bada Mako 2 A Sake Wani Zaben
- Za A Kira Taron WIC Na 2022 A Garin Wuzhen Daga 9 Zuwa 11 Ga Watan Nuwamba
An gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu kan laifuka guda biyu na hada baki wajen aikata laifin kisan kai wadda aka gano gawar a wata tsohuwar rijiya da ke gidan.
Dansanda mai gabatar da kara Simon Wada, ya ce Cecilia ta hada baki da wasu mutane wajen yin kisan kai wanda su kuma wadancan mutanen tuni zakara ya ba su sa’a.
Haka kuma ya gaya wa kotun cewa Cecilia ya ba Stephen manja don ya sha da tsakar dare, wanda shi ne ya yi sanadiyyar mutuwar Stephen.
Mai gabatar da karar ya ci gaba da cewa, bayan aikata laifin, wadda ake zargin ta roki wadanda suka gudun sun taimake ta wajen fito da gawar Stephen daga cikin rijiya. Hukumar ta ce, har yanzu matar ba ta fadi dalilin kashe Stephen ba.
Wada ya ce, wannan laifin ya saba wa sashi na 516 da na 316 na dokar manyan laifuka ta jihar Ondo ta shekara ta 2022.
Lauyan wanda ake kara, Adedire, ya bukaci kotun ta dage sauraren wannan kara zuwa domin ya samu damar shirya bayanansa, sai mai gabatar da kara ya bukaci kotu ta bayar da umarnin tsare wanda ake tuhumar a kurkukun Olokuta, har zuwa lokacin sake gurfanar da shi.