Hukumar Yaki Da Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ta afka Jihar Jigawa tare da cafke tsohon kwamishinan al’amuran kananan hukumomi, Hon. Aminu Ahmed Kanta.
Kanta ya taba rike mukamin kwamishinan al’amuran kananan hukumomi, kwamishinan kasa da tsare-tsare da kuma mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa a gwamnatin gwamna mai ci Muhammad Badaru Abubakar.
- Dan Takarar Majalisar Wakilai A Jam’iyyar APC A Enugu Ya Rasu A Hatsarin Mota
- Da Dumi-Dumi: ASUU Ta Musanta Shirin Sake Shiga Yajin Aiki
LEADERSHIP ta tattaro tsohon Kwamishinan, wanda aka damke shi a ranar Litinin, an kai shi Abuja domin yi masa tambayoyi.
Kanta, wanda makusancin siyasa ne ga gwamna Badaru a halin yanzu dan takarar jam’iyyar APC ne a mazabar Garki/Babura a jihar a zaben 2023.
Duk da cewar EFCC ba ta bayyana dalilin kama shi ba har yanzu, amma hakan ba zai rasa nasaba da mukamin da ya taba rikewa ba.