Dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a zaben 2023 na jam’iyyar APC, Air Marshal Sadique Baba Abubakar (Mai ritaya) ya bai wa dalibai dari biyu da daya (201) tallafin karatu a bangaron kwasa-kwasan kiwon lafiya daban-daban a kwalejin koyon jinya ta Malikiyya da ke Bauchi.
Da ya ke jawabi yayin miki shaidar tallafin ga daliban da suka ci gajiyar, Sadique Baba Abubakar ya bayyana cewar kiwon lafiya sashi ne da ke da matukar muhimmanci ga al’umma, don haka ba za su yi sako-sako da harkar da ta shafi lafiya ba.
Dan takarar ya jinjina tare da yaba wa kokarin Dan-Malikin Bauchi, Alhaji Aminu Muhammad bisa samar da makarantar koyon jinya mai zaman kanta a jihar da ke maida hankali wajen koyar da dalibai ilimin kiwon lafiya daban-daban.
Ya kuma nuna gamsuwarsa bisa yadda tsarin zubin makatatar yake tare da nuna cewa akwai bukatar a karfafi mutanen da ke kawo irin wannan cigaban a jihar ta Bauchi.
“Abun takaici ne a ce an fara tunanin kafa wannan makararta ne da cewa za a yi hadin guiwa da Gwamnatin jiya amma daga karshe Gwamnatin ta zame ta bar Dan Maliki shi kadai.
“To alhamdullahi wannan abun da Dan-Malikin Bauchi ya ke yi ya sanya asasin gina al’umma ne.”
Ya ce, ilimin da daliban ke samu ba kawai ma zallar taimaka musu yake ba, yana kuma taimaka wa hukumomi wajen tabbatar da kiwon al’umma.
Ya bada tabbacin cewa za su ci gaba da taimaka wa mamallakin makarantar domin kyautata koyo da koyarwa a bangaren kiwon lafiya. Ya ce, babu wani abun da ya fi lafiyan jama’a, don haka ya ce duk abun da aka zuba a bangaren lafiya ba asara aka yi ba.
Ya jawo hankalin daliban da suka ci gajiyar tallafin ilimin da su maida hankali su koyi ilimin da ya dace domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Ya kuma daura da cewa za su yi zama na musamman da mai makarantar domin ganin hanyoyin da za su bi wajen ingantawa da bunkasa makarantar domin cigaban dalibai, jama’a da kuma inganta sashin kiwon lafiya a jihar.
Tun da farko da ya ke jawabin maraba, Mai mallakin kwalejin, Alhaji Aminu Muhammad ya ce an kafa kwalejin Malikiyya ne da zimmar shawo kan gibin da ake da shi na karancin jami’an kiwon lafiya a asibitin da ke jihar.
Ya ce, su na koyar da kwasa-kwasai da sama a bangaren kiwon lafiya, kuma zuwa yanzu makarantar tana da dalibai sama da 3,000.
A cewarsa kwalejin tana da lasisi da amincewar hukumomin da ke kula da sashin gami da fatan cewa nan gaba za su cimma muhimman nasarori.