Wannan shi ne ci gaban maudu’in da aka fara bugawa makon daya gabata mai taken“Hanyoyin kula lafiya lokacin Hunturu wato Sanyi”.
Sa kayayyakin da suka kamata
Yana da matukar kyau kayan da suka dace da shi yanayiun na Sanyi ko Hunturu, wadanda ba za su ka kamu da Sanyi ba ko fatar jikin mutum ta bushe.
Kamar irin kayan da za su rika rike dumi daga jikin mutum da rage dumin da zai fita.Hakanan ma mutum zai rika sa safar Hannu da kuma Takalmi kafa ciki domin tabbatar da kasancewa cikin dumi.Ana ma iya sa Tabarau don kare ko hana kura shiga cikinsu, saboda idan kura ta shiga hakan kan iya sa Idanu su yi ja da kuma kaikayi.
Kulawa da fatar wajen kar a bari ta bushe
Lokacin da ake fama da Sanyi mutane da yawa suna fama da matsalar tattarewar fata da bushewar ta musamman lebe da bushewar fata.Wadannan shawarwarin zasu taimakawa wajen kare fata ta kasance ba matsala da rashin bushewa.
Domin hana fatar jiki bushewa sai ayi amfani da man shafawa da ke gyara fata, saboda bada bata lokaci bane zasu shiga cikin fata su hanata bushewa.Wadanda ya dace ayi amfani dasu sun hada da olibe oil da kuma shea butter.
Shi Olibe oils ya kunshi sinadaran fatty acids masu yawa, sun dace ayi amfani dasu a fatar jiki don hanata bushewa.
Shi Shea butter yana amfani ne wajen sa fatar jiki tayi laushi da hanata bushewa, tana kare fatar daga kura, bushewa, da duk wani abinda zai cutar da fatar jiki.Hakanan ma shi sinadarin fatty acids dake cikin man butter, kamar linoleic, oleic,stearic da palmitic,suna taimakawa wajen kare fata.
Sa Zuma ka hada da lemons cikin kofi sannan ka zuba ruwan dumi
Wannan hadin yana aiki kwarai da gaske dangane da bushewar makogwaro da kaikayin shi.Yana aiki wajen bada sauki cikin sauri domin Zuma maganin Tari ce da Makogwaro Har ila yau Zuma ana iya zuba ta a kan snack ko a sa ta a Shayi ko Kofi gwargwadon yadda mutum yake bukata.
Nemi taimakon asibiti idan da bukata
Lokacin Sanyi ko Hunturu yana sa wasu mutane shiga matsalar kamuwa da rashin lafiya, kamar cutar Asma,Hamma,da kuma Tari. Akwai yawan kura,ga zazzabi mai zafi, wanda yake sanadiyar jin kaikayi,ko ciwo, a hanyar da iska take wucewa,wannan na iya samar da wata babbar matsala.Idan har an ji irin wadannan alamun lokacin Sanyi sai aje Asiniti domin samun taimakon daya dace.