Ka bar maganar dabbar ruwan nan da ake kira ‘blue whales’ da Ingilishi da manya-manyan bishiyoyin jan katako. Babbar halitta mai rai da aka sani, ta kai girman fadin sama da mil biyu, kuma da wuya ka tada ganinta.
Kwararran kukun nan (mai dafa abinci) na kasar Italiya Antonio Carluccio ya ce tana da dadi sosai idan aka ci ta da taliya da kuma jan barkono. Amma kuma a wajen masu lambu barazana ce ga furanninsu da sauran abubuwan da suke shukawa.
- Kwanturola-Janar Na NIS Ya Amince Da Nadin Tony Akuneme A Matsayin Sabon Kakakin Hukumar Na Kasa
- Adabin Zamanin Da Na Sin (3)
Wannan halitta ta shuka (honey fungus) wadda wani nau’i ne na abin da wasu ke kira naman gwari ko naman kaza (mushroom), ba raba kan masana kawai ta yi ba, ana kuma yi mata kallon halitta mai rai da ta fi girma a doron duniya.
A takaice ita wannan shuka da ake kira da harshen Inglishi ‘honey fungus’ a fadi ta kai girman mil 2.4 ko kilomita 3.8 a yankin Blue Mountains na Oregon da ke Amurka.
Nau’uka daban-daban na wannan tsiro (fungi) da aka fi sani da sunan na Ingilishi ‘honey fungus’, suna kashe bishiyoyi da sauran shukoki na katako (manyan bishiyoyi) da yawa.
Tarin tsirran wannan halitta da ake gani a kan kasa (fili), wani sashe ne na ‘ya’yan itace na wannan shuka mai girman gaske da ke karkashin kasa.
Duk tsawon lokaci sai a ‘yan shekarun nan ne masana kimiyya suka gano yadda girman wannan shuka yake.
Mai kashe bishiyoyi:
A shekarar 1998 wani ayarin ma’aikatar kula da gandun daji ta Amurka, ya shiga binciken dalilin da ke sa wasu bishiyoyi masu yawa suke mutuwa a gandun dajin
Malheur da ke gabashin Oregon.
Masu binciken sun gano yankin da abin ya shafa ta hotunan da suka dauka ta jirgin sama, kuma suka tattara samfur na bishiyoyin da suka mutu da kuma wadanda suka kusa mutuwa har 112. Binciken da aka yi ya nuna dukkanin bishiyoyin in banda hudu wannan shuka ce (armillaria solidipes) ta kama su.
Idan wata saiwa ta wannan shuka ta hadu da wata wadda suke da irin kwayoyin halitta iri daya, sai su hade su haifar da shuka daya.
Masanan sun yi amfani da wannan ilimi, wajen sanin wadanne ne suke hadewa kuma wadanne ne ba sa hadewa, daga nan sai suka gano cewa tarin saiwa iri daya masu kwayoyin halitta iri daya ne suka harbi bishiyoyi 61 daga cikinsu (wadanda suka mutu da wadanda suka kusa da mutuwar).
Tsakani mafi girma daga shuka daya zuwa wata shukar ta wannan tsiro ko halitta shi ne mil 2.4 ko kilomita uku 3.8.
Masu binciken sun yi lissafi suka ga wannan shuka (Armillaria solidipes) ta yadu a filin da ya kai fadin murabba’in mil 3.7 ko kilomita 9.6, kuma ta kai tsakanin shekara 1,900 da 8,650.
A wannan lokaci kafin a gano wannan ta yanzu, halittar da aka sani mafi girma a duniyar, ita ma shuka ce wadda suke nau’i daya, wadda aka gano a 1992 a Kudu maso Yammacin Washington, ita kuma ta yadu har zuwa fadin murabba’in sama da kilomita shida da rabi.
Masana ilimin halittu sun dade suna muhawara a kan mizani ko ma’aunin da za a yi amfani da shi wajen ayyana halitta guda daya, wato a ce wannan halitta zaman kanta take yi, ita kadai ce ba ta yi tarayya da wata ba.
A kan haka ne ita wannan shuka, ta cimma wannan matsayi na zama halitta daya mai zaman kanta saboda gaba dayan wannan fili da ta mamaye a karkashin kasa dukkanin saiwowin suna da kwayar halitta iri daya ne, sannan suna iya sadarwa tsakaninsu, wanda hakan ke nuna suna da manufa daya ko kuma akalla suna aiki tare.