Gwamnatin Holland za ta haramta amfani da sinadarin iskar da ke sa mutane jin wasai su daina jin damuwa tare da sanya su kyalkyala dariya, wanda ake kira da Ingilishi Laughing Gas ko kuma Nitrous Odide a kimiyyance.
Hukumomi za su dauki matakin ne sakamakon illar da ake ganin zai iya yi ga lafiyar matasa wadanda ke ta shiga dabi’ar amfani da shi.
- Da Dumi-Duminsa: Buhari Ya Tsige Fadah A Matsayin Darakta Janar Na NYSC
- Adabin Zamanin Da Na Sin (3)
Haramcin wanda zai fara aiki daga watan Janairu, zai sa daga lokacin ya zama laifi a sayar ko saye ko kuma mallakar sinadarin. Sai dai kuma hukumomin sun ce za a iya amfani da shi a bangaren kula da lafiya da kuma fannin kamfanonin hada kayan abinci.
Gwamnatin na fatan haramcin zai sa a samu raguwar yawan hadarin ababen hawa a tituna, wadanda amfani da sinadarin kan janyo.
Kiyasin wata kungiya mai fafutukar kare hadura a kasar ta Netherlands, TeamAlert, sinadarin ya taka rawa wajen haddasa haduran ababen hawa 1,800 a fadin kasar a cikin shekara uku da suka gabata.
Kusan a duk kwana biyu ana samun hadarin da ke da alaka da amfani da iskar, lamarin da ya tayar da hankali, in ji Maartje Oosterink ta kungiyar.
Sinadarin wanda kafin wannan matakin ba laifi ba ne amfani da shi, yana samun karbuwa tare da amfani da shi sosai a tsakanin masu zuwa gidajen rawa da tarukan holewa da liyafa.
Kuma yawanci akan yi amfani da shi ta hanyar surka shi da wasu miyagun kwayoyin.
Galibi ana sayar da iskar sinadarin ne a cikin wani dan karamin gwangwani, inda ake durewa a cikin balan-balan kafin a rika shaka.
Wani bincike da wata cibiya, Trimbos Institute, ta gudanar ya nuna cewa sama da kashi 37 cikin 100 na masu zuwa gidajen rawa da liyafa a kasar ta Holland suna amfani da sinadarin kusan a ko-da-yaushe, wadanda kuma yawanci matasa ne.
A yanzu hukumomi na nuna matukar damuwa a kan illa ko tasirin da sinadarin ke da shi a cikin kwakwalwa da kuma jikin dan’Adam.
Bincike ya nuna cewa yawan amfani da sinadarin ka iya haifar wa da jikin mutum karancin sinadaran bitamin, wanda kuma hakan ka iya lalata wani bangare na jikin mutum ko shanyewar barin jiki.
Amfani da sinadarin domin nishadi na haifar da gagarumin hadari ga lafiya in ji karamin sakataren lafiya da wasanni da kuma jin dadin jama’a na kasar, Maarten ban Ooijen a lokacin da yake bayyana haramcin. Haramcin za isa daga lokacin ‘yan sanda su kama duk wanda suka samu gwangwanin sinadarin a cikin motarsa, in ji ministan shari’a Dilan Yeşilgöz.
Fargabar yadda ake samun karuwar masu amfani da sinadarin ta wuce kasar ta Netherlands kadai.
A Ingila sinadarin ne aka fi yawan amfani da shi a cikin miyagun kwayoyi bayan ganyen Wiwi a tsakanin matasa masu shekara 16 zuwa 24.
A watan da ya gabata ma’aikatar cikin gida ta Birtaniya ta fuskanci yawan kiraye-kiraye kan ta haramta sayar da shi haka sakaka a titi ga jama’a saboda yadda ake samun karuwar masu amfani da shi ta yadda bai dace ba.
Ana samun sinadarin barkatai domin amfani da shi don nishadi, saboda ana iya sayensa a ka’ida ko a sayar domin amfani da shi wajen yin askirin.
Ana yawan amfani da shi a manyan tukwanen gas a matsayin sinadarin kashe zafi ko radadi idan marasa lafiya suka shake shi a asibiti da kuma wadanda za a yi wa aikin tiyatar hakori.
Mun Ciro muku daga BBC.