Assalamu alaikum iyaye barkanmu da warhaka, sannunmu da arzikin sake haduwa a cikin wannan fili namu mai farin jini da albarka raino da tarbiyya.
A wannan lokaci da muka fara shiga cikin yanayi na iskar sanyi da hunturu yana da kyau iyaye mu kula da yaranmu kwarai wurin tabbatar da basu samu matsalar kamuwa da sanyi ba.
- 2023: Gudummawar Da Ya kamata Jami’an Tsaro Su Bayar
- Da Dumi-Duminsa: Buhari Ya Tsige Fadah A Matsayin Darakta Janar Na NYSC
A wannan lokaci yara suna bukatar dumi, wanda hakan ba zai samu ba har sai an tanadar musu da kayan sanyi, hula, safa, da kuma yin amfani da dogayen wando.
Mu sa ido da hanasu yin wasan kasa don gujewa kamuwa da mura, haka kuma wasan kasa na bata kaya da saurin haifar da datti a tufafi.
Ban da yi musu wanka da dare ko da Sanyin safiya, gudun haifar musu da matsala. In za a yi musu wanka da safe a tabbatar ruwan ba da zafi a kuma yi musu a bandaki me rufi, son samu a yi musu wanka da rana misali da azahar, a hakura da yi musu ba na dare domin a lokacin akwai iska me sanyi da ke kadawa.
Haka mu guji barinsu fita da dare ko da Sanyin safiya, son samu duk aikar da za a yi musu a yi shi da yamma kafin magriba in har kuma ya kama dole sai sun fita to a tabbatar da kayan sanyi a jikinsu.
Allah ya bamu Ikon yi, ya sa mu gyara.