Kamar yadda na yi bayani a makon daya gabata cewa lokacin Sanyi wasu mutane suna mayar da kansu,ko gaba daya ma su kasance kazamai.
Domin kuwa da zarar an kaurace ma yin wanka shikenan wasu cututtuka kamar su Kazuwa sun samu damar shiga cikin jiki ke nan.Shi yasa Maigida abinda aka fi so daga gare shi shine ya dauki kwararan matakai, da za su taimaka ma shi kasancewa cikin halin lafiya lokacin Hunturu.
A tuna ita Kazuwa idan ta riga ta shiga cikin iyali ta kuma yi dace kazanta tana nan renonta ma ake yi, maimakon yaki da ita.Shike nan sai abinda hali yayi kuma
Sanin kowa ne akwai cututtukan da su kan yi tasiri lokacin Sanyi ko Hunturu kamar su Asma,Mura, Mashako,da dai sauransu. Duk idan su matakan da suka dace a dauka aka kasa daukarsu ko shakka,babu da akwai yiyuwar kamuwa da daya daga cikin cututtukan shi yasa ake cewa idan kunne ya ji gangar jiki ta tsira.
A kuma tuna son zuciya daga karshe shine ke zama bacinta domin kuwa da farko za aji dadi na wani lokaci da ba dadewa za ayi ba,saboda an ba ita zuciyar abinda take so,amma daga baya kuma idan ta fara biyan adashi sai fa an an karba ko ba a so kwasa ba,ba makawa sai an shiga matsala.
Bugu da kari lokacin Sanyi akwai wani abin da yak an damu wadansu mutane da ake kira da suna Faso,inda kasan kafa zai yi Faso inda zai tsage wani lokaci ma har jini ya kan yi.Wannan babbar matsala ce da take daukar mataki ba na bata lokaci ba,saboda wasu cuta ce dasai lokacin Sanyi take tashi.Wasu tsananin rashin kulawa da jikinsu ne yake sa hakan.
Maigida ya dace ya dauki matakan da suka kamata wajen samar da kayan da suka dace musamman yara, su rika sawa lokacin Hunturun kai har ma da manya.Takalma wadanda ake kira kafa ciki suna maganin shigar Sanyi ta kafa akwai bukatar tanadar su, da duk wadansu matakan da za su hana galabaita a lokacin da Hunturu yake gaiyarsa.