Mata masu sarrafa rogo da Kwakwar Manja zuwa sauran nau’ukan abinci a jihar Binuwe sun koka kan yadda suke sha bakar walaha wajen sarrafa amfanin ta hanyar yin amfani da Gawayi da Itace, inda suka ce, hakan ke sanyawa hayaki ya cika masu idanuwan.
Daya daga cikin su wata uwargida mai suna Onyeka Audu ta sanar da cewa, ba ta yin wata sana’ar wadda ta wuce ta sarrafa garin rogo da kwakwar manja zuwa sauran nau’ukan abinci, ida ta ce, ba mu da karfin da za mu yi amfani da wutar lantarki ko kuma kayan aiki na zamani don yin aikin a cikin sauki.
- Peng Liyuan Ta Ziyarci Dakin Adana Kayan Tarihi Na Fasaha Na Birnin Ayutthaya Na Thailand
- 2023: INEC Ta Nemi Masu Kada Kuri’a Da Su Duba Sunayensu Cikin Wadanda Ta Yi Wa Rajista
Ba wai Onyeka ba, haka sauran mata da ke yin wamnan sana’ar, suma suna fuskantar wannan kalubalen, musamman a karamar hukumar Okpokwu wadanda keda alummar da suma kai yawan 237,000
Suk da cewa, Nijeriya ta shiga cikin sahun tsarin muradin karni, musamman domin yin amfani da makamashi nan da shekarar 2030nan.
Bankin duniya a cikin watan Afirilun shekarar 2021 ya an dora kasar a kan sikilen kasashen da ke da alumma mai yawa, amma sai dai, abin takaici, kasar ta kasance ta na fama da raahin wadacacciyar wutar lantarki.
Har ila yau, hukumar samar da wutar lantarki a karkara REA ta kiyasata cewa, akalla a cikin yawan alummar kasar nan miliyan 200 a cikin wannan adadin da miliyan 100 ne ke samun wutar lantarki, inda hakan ke kara ta’azzarar haifar da yunwa a kasar.
A wani rahoton da hukumar ta fitar a shekarar 2017 tya sanar da cerwa, kashi 36 a cikin dari na alummar da ke zaune a cikin karkara a kasar nan ke samun wutar lantark, inda kuma kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 95 ke samun wutar ta lanrakin.
A wani rahoton bincike da aka wallafa na NDHS a shekarar 2018 wanda kuma hukumar kidaya ta kasa ta aminta da shi, an bayana cewa, akasarin wadanda ba su da wutar ta lantarki, na zaune a cikin karkara.
Misali, al’umomin a jihar Biniwe garin Ugbokolo an sada shi da babban layin wutar lantarki na kasa.
Har ila yau, a bisa wani bincike da aka gudanar, an gano cewa, mata da yara da ke taya iyayn su aikin na sarrafa Rogon da kuma Kwakawar ta Manja, sune suka fi shan wahala saboda hayakin da ake sarrafa wadanan amfanin biyu.
A bisa wani bincike da aka yi a yankunan Ihem, Okonobo, Odessassa, Mabe, Aikpla, Effoyo da kuma a karamar hukumar Okpoga in Okpokwu L da ke a cikin jihar ta Binuwe, mata da maza sun fi yin sana’ar ta sarrafa Rogon da Kwakwar Manjan zuwa sauran nau’ukan abinci.
Wata mazauniya a yankin Ihem Kate Onche ta sanar da cewa, tana yin amfani da itace ne domin sarrafa rogon da kwakwar manjan, inda ta ce, tana sarrafa buhun garin mai cin kilo 50.
Ita ma wata mai sarrafa kwakwar manja a yankin Aikpla Mary Adoga ta sanar da cewa, rashin wutar ta lantarkin, na janyo masu cikas, inda ta sanar da cewa, sai sun tara itace da yawa ne suke iya gudanar da aikin
Mary Adoga ta kara da cewa, idanuwan sun a yi masu zafi saboda hakin na itacen haka sukan fuskanci ciwon kai mora da saurans.u
A cewar Mary Adoga, “rashin wutar ta lantarkin, na janyo masu cikas, inda ta sanar da cewa, sai sun tara itace da yawa ne suke iya gudanar da aikin”.
Hakazalika, ita ma wata mai suna Paul Olomu ta bayyana cewa, idanuwanta sukan yi ciwo saboda hayakin na itacen da suka yin aikin sarrafa Garin ko kuma Kwakwar manjan
Bincike ya nuna cewa, masu aikin ‘yan kadan ne daga cikin su ke yin amfani da man Dizil don gudanar da aikin na sarrafa Rogon da kuma Kwakwar manjan, inda akasarin mata da suke yin wannan sana’ar, suka dogara kachokam a kan yin amfani da itace
A bisa wani bincike a watan Yulin shekarar 2022 da hukumar kiwon lafiya ta duniya ta gudanar WHO a akan shakar gurbatacciyar iska ta bayyana cewa, kashi 32 a cikin dari na mutane na kamuwa da cututtuka, inda kuma mutane kashi 12 a cikin dari ke mutuwa saboda shakar gurbatacciyar iskar.
A cewar binciken, kashi 12 daga cikin dari na mutane na mutuawa ne saboda hayakin itace da na kalamzir da sauransu.