Masu bibiyar wannan shafi barkan mu da sake haduwa a wannan makon. A yau za mu tattauna ne a kan wasu muhimman abubuwa biyu da suke damun wasu mata sosai.
Su ne yadda hammata ke yin baki da kuma yadda su ma cinyoyi ke rikidewa su yi baki.
- Sin Ta Zama Misali A Fannin Inganta Ci Gaban Kasa Da Kasa
- Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali Su Ne Muradun Sinawa
A kan samu wasu matan masu fama da bakin hammata da cinyoyi, musamman idan suna gugar juna. Idan kina da irin wannan matsalar, share hawayenki, na tanadar muku da tsarabar musamman na magance wannan.
Abu na farko da uwargida za ta yi bayan askin gashin hammata shi ne, ta shafa man zaitun, ka da ta shafa hoda, domin hoda na sanya wajen ya yi baki. Bayan an shafa zaitun din za a bari har na tsawon kwana uku. Daga nan ba za a shafa komai ba, duk sanda uwargida ta yi wanka, ba za ta kara shafawa komai ba, sai turare. A rana ta uku sai ta nika Cocumber, ta shafa ruwan a hammata, kafin ta shiga wanka. Ta bar shi har sai ya bushe, ta shiga wanka. Bayan ta fito, sai ta kara shafa zaitun din. Haka ma za a rika shafawa tsakanin cinyoyi.
A kula, bin wadannan ka’idojin yana da matukar amfani, don haka uwargida ta daure ta bi su daki-daki.