Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya taya tsohon shugaban kasa Dakta Goodluck Ebele Jonathan murnar cika shekaru 65 a duniya, a madadin gwamnati da ‘yan Nijeriya.
Shugaba Buhari a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya fitar, ya bayyana matsayinsa na musamman da tsohon shugaban kasar yake da shi wajen ci gaban kasa, tare da sadaukarwa da kuma samun nasarar sace zukatan ‘yan Nijeriya da kuma al’ummar kasar nan a matsayinsa na mai zaman lafiya, ta hanyar ci gaba da gadar da sulhu da kishin kasa a kasashe da dama.
- Xi Jinping Ya Ci Gaba Da Halartar Taron Karba-karba Na Shugabannin Mambobin Kungiyar APEC Karo Na 29
- Hadari Gabas…Yadda Tattaunawar Tinubu Da Atiku Lokacin Da Suka Hadu A Abuja Ya Gudana
Shugaban ya bi sahun ‘yan uwa, musamman matarsa, Patience da mahaifiyarsa Eunice, wajen murnar wani gagarumin ci gaba a rayuwar tsohon shugaban, inda ya tuna tafiyarsa ta siyasa, wadda a bayyane ta ke ya kasance mai kishin kasa wanda ya fara a matsayin mataimaki.
Ya yi Gwamna daga 1999 zuwa 2005, ya saje yin Gwamna daga 2005 zuwa 2007, sai mataimakin shugaban kasa, dava 2007 zuwa 2010 da kuma shugaban kasa, daga 2010 zuwa 2015.
Shugaban ya yi imani da zumunci, aminci, da tawali’u na Dakta Jonathan na ci gaba da bude damar yin hidima ga bil’adama tare da bayyana hanyar da tsohon shugaban kasar zai iya saka hannun jari a cikin mutane, cibiyoyi, da kasashe.
Yayin da Jonathan ya cika shekaru 65, shugaba Buhari ya yi addu’ar fatan alheri a gare shi da ma iyalansa.