Kimanin makonni biyu wasu ‘yan daba sun kai wa ayarin motocin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar hari a Jihar Borno, an sake kai wa magoya bayansa hari a Jihar Gombe.
An tattaro cewa akalla mutane uku ne suka samu raunuka daban-daban a ranar Litinin tsakanin ‘ya’yan Kalare da magoya bayan Atiku a lokacin yakin neman zabensa a Jihar Gombe.
- Lalong Ya Gana Da Shugabannin Al’umma Kan Yawan Kashe-Kashe A Filato
- Girgizar Kasa Ta Kashe Mutum 56 Ta Jikkata Daruruwa A Indonesia
Rikicin ya yi sanadiyar lalacewar motoci uku da suka hada da mota kirar bas da kuma babur mai kafa uku guda daya mallakin magoya bayan Atiku.
Rahotanni sun ce an yi wa magoya bayan kwanton bauna ne a filin wasa na Pantami.
A cewar wata majiya, yaran Kalare dauke da makamai sun afkawa magoya bayan jam’iyyar da ba su ji ba gani, wadanda ke kan hanyar zuwa gidajensu bayan tashi daga taron.
Da aka tuntubi kakakin ‘yansandan Jihar, ASP Mahid Abubakar domin jin ta bakinsa, ya ce yana cikin wani taron bita kuma bai tabbatar da faruwar rikicin ba.