Asusun bayar da lamuni na duniya (IMF) ya bayyana cewa Nijeriya za ta iya fuskantar mummunar hatsarin karancin abinci da a 2023, sakamakon ambaliyar ruwa da kuma tsadar takin zamani.
A cewar hukumar kididdiga ta kasa (NBS), an samu karuwar farashin kayayyakin abinci na kashi 23.72 a shekara bayan shekara har zuwa watan Oktobar 2022, inda a yanzu ake samun hauhawar farashin kayayyakin abincin a tsakanin kashi 50 zuwa 100.
- Gudummawar Kamfanonin Fasahar Sadarwar Kasar Sin Ga Kara Dunkulewar Duniya
- Kasashen Turai Sun Fusata Da Matakin Amurka
Duk da hasashen IMF kan ambaliyar ruwa da aka samu a damunan bana wanda ta shafi harkokin noma, ya de za a samu mummunan tashin gwauron zabi na kayayyakin abinci a 2023.
Ya kara da cewa sakamakon sauya fasalin naira da gwamnatin tarayya take ci gaba da kare babban bankin Nijeriya (DBN) wajen samun kudade da za su dike gibin kasafin kudi da kuma rage hatsarin sauyin yanayi.
IMF ya bayyana hakan ne a cikin wani rahoton 2022 wanda ya gudana a makon da ya gabata.
Ya de, “Sakamakon matsalolin da ambaliyar ruwa ta haddasa wanda ya janyo hauhawar farashin takin zamani da tagayyara harkokin noma, wanda hakan na iya ta’azzara hauhawar farashin kayayyakin abinci a 2023.
“Bugu da kari, sauya fasalin kudi a kasuwar canji wanda DBN ke di gaba da dogaro a kai da zai dike gibin kasafin kudi zai kara hauhawar farashin. A dikin dan karamin lokadi, zai haddasa barazana a bangaren farashin mai da canjin sanayi, yayin da shi ma barazanar sauyin yanayi zai haddasa barazana ga harkokin noma a Nijeriya.”
A cewar IMF, duk da karandin matakan da Nijeriya ke dauka, yakin Ukraine ya shafi kasar wajen farashin kayayyakin abindin gida. IMF ya de karancin abinci zai iya shafar Nijeriya ta hanyoyi da dama.
IMF ya kara da cewa nan da shekaru 10 masu zuwa dole ne Nijeriya ta samar da karin guraban ayyuka guda miliyan 25. Ya de bangaren harkokin noma yana matukar samar da ayyukan yi da abindi da warware matsalolin zamantakewa.
A ranar Alhamis da ta gabata de, hukumar NBS ta bayyana cewa ‘yan Nijeriya miliyna 133 ne ke fama da kangin talauci, wanda akwai bukatar kasar ta samar da abinci da kula da lafiya da kuma harkokin ilimi.