Dan takarar shugabancin kasar na jam’iyyar APC a zaben 2023, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya shawarci manyan abokan karawarsa, Atiku Abubakar da Peter Obi da su hakura su bar masa neman shugabancin kasar nan.
Tinubu, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a a masarautar garin Gbaramatu da ke karamar hukumar Warri a kudu Maso Yamma, ya ce, Atiku wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya jima lokuta da dama yana neman kujerar ba tare da ya samu nasara ba, don haka da bukatar ya janye muradinsa na sake neman a 2023.
- Zamanintar Da Sha’anin Gona Da Kauyuka Ya Dogaro Da Halin Da Ake Ciki Da Muradun Jama’a
- Ko Kun San Gida Mafi Tsada A Duniya?
Da ya ke magana da Pere na Gbaramatu, Oboro-Gbaraun II, Aketekpe, Agadagba da kuma dandazon magoya bayansa a masarautar Basaraken, Tinubu ya ce: “Sau nawa Atiku na neman mulkin nan? Ko da yake Atiku na kan nema, ku fada masa ya koma gefe kawai ya zauna, hakan ya isa.”
Kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP), Peter Obi, Asiwaju Bola ya ce, lissafin kididdigar Obi da nazarinsa kan tattakin arziki dukkaninsu cike suke da tukin kuskure.
“Ba na son jero sunaye, yana tunanin kididdigar da zai bai wa ‘yan Nijeriya abinci ne? Ya na bada kididdiga marar kyau, tattakin arziki marar kyau. Ba wannan al’ummar Nijeriya ke bukata ba,” Tinubu ya fada wa Obi.
Tinubu, wanda aka nada masa Sarautar Iyelawei na masarautar Gbaramatu Kingdom da Sarkin ya ba shi, ya sha alwashin cika dukkanin alkawuran da ya yi, ya kuma yi alkawarin samar da abubuwan cigaba ga al’ummar Gbaramatu, musamman a bangaren shimfida titina, Jami’a, da sauransu, ya ce ba zai taba yin nisa da masarautar ba.
“Zan ci gaba da neman shawarorin Sarki domin cigaban masarautar Gbaramatu, don yin aiki wajen bunkasa tattalin arziki”.
Wadanda suka yi wa Tinubu rakiya sun hada da gwamnonin Kano, Abdulahi Ganduje, Mai Mala Buni na Yobe; karamin ministan albarkatun Mai, Timipre Silva; karamin ministan kwadago, Festus Keyamo; Dimeji Bankole, da tsohon ministan kula da harkokin Niger Delta Affairs, Elder Godsday Orubebe, da sauransu.