Hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda sabuwar zanga-zangar adawa da kullen korona ta ɓarke a birnin Urumqi na ƙasar China.
BBC ta rawaito cewa, Zanga-zangar ta ɓarke ne bayan da wata gobara da ta tashi a wani gini ranar Alhamsi ta kashe mutum 10 a birnin.
- Dan Bindiga Ya Kashe Kananan Yara ‘Yan Makaranta 36 A ThailandÂ
- Yobe Ta Arewa: APC Ta Sha Alwashin Daukaka Kara Kan Nasarar Machina A Kotu
An ga masu zanga-zangar na fuskantar jami’an tsaro, yayin da suke karya shingayen da aka kafa tare da ihun ”a kawo Æ™arshen kullen korona”.
To sai dai hukumomin birnin na Urumqi sun musanta zargin cewa dokar kullen ce ta hana mutanen kuɓucewa gobarar.
Birnin wanda ke yammacin ƙasar na cikin dokar kullen korona tun farkon watan Agusta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp