Ma’aikatar ma’adinai da karafa ta kasa, ta ce shirin hada-hadar Zinari (Gold Souk) ta Kano da sauran shirye-shiryen ci gaba na yankuna da ma’aikatar ke aiwatarwa za su fara aiki nan da shekarar 2023.
Ministan ma’aikatar, Olamilekan Adegbite ne ya bayyana hakan a lokacin da yake wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) a Abuja.
Adegbite ya ce hada-hadar zinarin za ta maida kasar Nijeriya ta zama kasaitattar Kasuwar zinari.
Ministan ce gwamnati ta horar da mutanen da za su kera kayan adon (sarka da dankunne) wanda za su kasance ‘yan kasuwar zinarin ne.