Dakin kwanan dalibai mai suna Benji ya kama da wuta a yau Juma’a, inda aka yi asarar abubuwa da dama a dalilin tashin gobara.
Leadership Hausa ta zanta da wani dalibin makarantar wanda gobarar ta faru a gaban shi, mai suna Musa Yusuf Mahogany, ya shaida cewa wutar ta tashi ne a daidai lokacin da ake sallar Juma’a.
- Yadda INEC Ta Bankado Wasu Mutane Da Daruruwan Katin Zabe
- LP, Ta Kori Daraktan Yakin Neman Zaben Obi, Okupe Da Wasu 11 Kan Gaza Biyan Harajin Jam’iyyar
Dalibin ya kara da cewa wutar ta kara tashi ne a dalilin bindiga da tukunyar girkin gas ta yi.
Ya cewa a daidai lokacin da wutar ke tsakiyar ci, sai motar ‘yan kwana-kwana ta bayyana don kai dauki.
Cikakken bayani na tafe…