• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mayakan ISWAP Da Boko Haram Sun Tafka Kazamin Fada A Tsakaninsu

by Sadiq
3 years ago
ISWAP

Rikicin da ya barke tsakanin bangaren mayakan Boko Haram da ISWAP, wanda aka ce an kashe ‘yan ta’adda da dama a cikin kwanaki ukun da suka gabata.

Zagazola Makama, kwararre kan yaki da tada kayar baya a yankin tafkin Chadi, ya tattaro cewa fitaccen shugaban kungiyar Boko Haram, Ali Ngulde, a ranar 3 ga watan Disamba, ya jagoranci daruruwan mayaka dauke da muggan makamai daga tsaunin Mandara, inda suka kai farmaki kan sansanin ISWAP a wani gagarumin farmaki da suka kai musu.

  • An Fitar Da Rahoton Masana Kan Ra’ayin Kare Hakkin Dan Adam Na Sin
  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Kwamishina A Binuwai Da Yin Awon-Gaba Da Wasu Mutum 3

Kazalika majiyoyin leken asiri sun shaida wa Makama cewa an fara arangama ne a sansanin Yuwe, wanda ya haifar da kazamin musayar wuta da mayakan Ngulde suka yi galaba a kan mayakan ISWAP tare da kashe 12 daga cikinsu sannan suka kwace makamansu.

Ba da jimawa ba, majiyoyi sun ce mayakan na Boko Haram sun yi gaggawar tattara karin mayakan daga sansanin Abu Ikilima da ke Gaizuwa, Gabchari, Mantari da Mallum Masari.

A cewar kwararre na yaki da ‘yan ta’addan, an kashe mayakan ISWAP sama da 23 a ranar 4 ga watan Disamba, lokacin da bangaren Shekau na kungiyar Boko Haram suka rabu gida biyu, suka kai farmaki kan ISWAP a Ukuba, Arra da Sabil Huda.

LABARAI MASU NASABA

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

Zagazola ya kara da cewa, a daren Lahadi, an ga wata tawagar mayakan da ke sansanin ISWAP a kusa da Kawuri da Aulari, inda a safiyar ranar Litinin wani babban shugaban ISWAP, Ba’ana Chingori, ya jagoranci wata tawagar mayakan da suka kai farmaki kan mayakan Boko Haram.

Rikicin da ya barke tsakanin bangarorin ‘yan ta’addar ya yi sanadiyar mutuwar mayaka da dama.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji
Manyan Labarai

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI
Manyan Labarai

Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

October 25, 2025
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka
Kiwon Lafiya

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025
Next Post
Yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya Na Bukatar Agajin Gaggawa – MDD

Yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya Na Bukatar Agajin Gaggawa - MDD

LABARAI MASU NASABA

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Yi Liyafar Murnar Kebe Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 25, 2025

Nafisa Abdullahi Aminu: Yarinyar Da Ta Ɗaukaka Darajar Nijeriya A Idon Duniya

October 25, 2025
Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

Sin Da Amurka Sun Fara Tattaunawa Kan Tattalin arziki Da Cinikayya A Kuala Lumpur

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus

October 25, 2025
Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

Firaministan Sin Ya Isa Singapore Don Ziyarar Aiki

October 25, 2025
Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

Gwarzuwar Hukumar Da Ta Kawo Sauyi A Kula Da Muhalli A 2025 Hukumar NASENI

October 25, 2025
An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

An Gudanar Da Taron Cika Shekaru 80 Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan Da Dawo Da Shi Kasar Sin A Beijing

October 25, 2025

Daɓid Adeyemi

October 25, 2025
Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

Wakilin Sin: Shawarar GGI Ta Nuna Yadda Za A Jagoranci Bunkasa Makomar MDD

October 25, 2025
Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka

October 25, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.