Babba jigo a kwamitin yakin neman zaben Jam’iyyar PDP a Jihar Sakkwato, Honarabul Aminu Bala Bodinga ya bayyana cewar jam’iyyar a Jihar ta fito da sabon salon yakin neman zabe ne domin kawar da matsaloli da kalubalen da jam’iyyar ke fuskanta domin samun nasarar Babban Zaben 2023.
Honarabul Aminu Bala wanda kuma shine Kwamishinan Filaye da Gidaje ya bayyana cewar sabon salon yakin neman zabe da suka bullo da shi mai tasiri ne da alfanu ga jam’iyyar PDP da al’ummar Jihar Sakkwato bakidaya.
Jigon dan siyasar ya bayyana hakan ne a yau a tattaunawarsa da manema labarai a wajen ci- gaba da taron masu ruwa da tsaki da jam’iyyar PDP ke gudanarwa da Karamar Hukumar Gudu a otel din Giginya.
Ya ce sabon salo ne suka fito da shi domin zama da kowace Karamar Hukuma a tattauna ido da ido a baje siyasa da matsalolinta a faifai akasin yadda ake yi a can baya. Ya ce a yanzu su kan zauna da dukkanin masu ruwa da tsaki a lamurran jam’iyya, a saurari matsaloli ta yadda wadanda ake iya gyarawa a gyara kai tsaye wadanda kuma ake alkawali sai a dauki alkawali zuwa bayan zabe.
Ya ce wani muhimmin lamari shine ko da akwai ‘ya’yan jam’iyya wadanda ke da sabani da juna, ba za a kammala taron ba sai an daidata su an fahimci juna, don haka ya bayyana cewar muhimmancin taron ya fi gaban a nanata.
“Tarukan da ake zuwa yakin neman zabe a Kananan Hukumomi shugabanni ne kawai ke samun damar magana ba tare da bayar da dama ga dukkanin jama’a su samu damar cewa wani abu ba, ko gabatar da korafi ba saboda rashin lokaci amma a wannan taron na masu ruwa da tsaki, akwai cikakken lokaci da damar sauraren kowa da kowa.” Ya bayyana.
“Misali a yanzu Karamar Hukumar Gudu ce muke zama da ita, kuma zaben 2019 da ya gabata mun samu gagarumar nasara a Gudu 100%, don haka a wannan zaben ma akalla muna son ka da mu kasa samun kashi 90% in sha Allah.”
A taron wanda Shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaben PDP a Jihar, Tsohon Ministan Sufuri, Honarabul Yusuf Sulaiman ya jagoranta ya bayyana za su aiwatar da kakkarfan kamfen din da zai tabbatar da samun nasarar jam’iyyar PDP a dukkanin matakai daga sama har kasa bakidaya.
A jawabinsa Mataimakin Dan Takarar Gwamnan Jihar Sakkwato, Honarabul Sagir Bafarawa ya bayyana cewar Karamar Hukumar Gudu ta jam’iyyar PDP ce gaba da baya don haka ba su da shakku a kan ta.
“Gudu ko kadan ba wajen zuwan APC ba ne, al’ummar Gudu bakidaya PDP suke yi domin ita ce jam’iyyar da suka yi amannar za ta rika kawar da matsalolin su da inganta jin dadin su.”