Wata babbar kotun jihar Ekiti, da ke Ado Ekiti ta yanke wa wani mutum mai kimanin shekara 24, mai suna Segun Iwaetan, hukuncin kisa ta hanyar rataya, saboda kama shi da laifin fyaden da ya yi wa wata makociyarsa mai shekara 20, da kuma kama shi da bindiga guda biyu.
An tuhumi wanda ake zargin ne da laifuka guda bakwai wadanda dukkansu ke da alaka da fyade da mallakar bindiga da kuma zama dan kungiyar asiri.
Kamar yadda takardar tuhumar ta nuna, “Segun Iwaetan da Atila Iwaetan (wanda a halin yanzu ya gudu), sun hada baki wajen balle gida da sata a shagon Olayemi Oyerinde, suka kwashi kaya wadanda aka kiyasta kudinsu fiye da naira miliyan 1.8.
Haka kuma wadanda ake zargin ya yi wa wata mace mai kimanin shekara 20 da ke zaune a Odo Ado, Ado Ekiti fyade, an kuma kama shi da laifin mallakar bindiga guda biyu da kuma laifin zama dan kungiyar asiri.
Wadda aka yi wa fyaden ta ce, “wannan da ya yi min fyadrn makocina ne. A wannan rana da zai yi min fyaden, sai ya shigo dakina da tsakar dare, ina kwance ya tashe ni, ya nuna min bindiga kuma ya ce, idan na yi ihu zai harbe ni. Sai ya ce in cire kayana , a nan ne ya yi min fyade. Bayan ya gama, sai ya roke ni cewa in yafe masa. Ni kuma na ce, na ki.”
Dansanda mai gabatar da kara, Albert Adeyemi, ya gabatar da shaidu guda biyar da suka tabbatar da bayanin wadda aka yi wa fyaden. Lauyan wanda ake zargin, bai kira shaida ko daya ba.
Da yake yanke hukunci, mai shari’a Adeniyi Familoni, bayan tabbatar da laifin da ake zargi, ya yanke hukunci kan hada baki wajen aikata laifi da mallakar makami ba bisa ka’ida ba, na shekara 12 a kurkuku, ba tare da zabin tara ba.
“Dangane da batun fyade kuwa, kotun ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai,” Sai kuma shiga kungiyar asiri ta Eiye, alkalin ya gaya wa wanda aka gabatar, cewa “hukunci na karshe shi ne na kisa ta hanyar rataya.”