An shiga tashin hankali a yankin Eha-Amufu da ke karamar hukumar Isi Uzo a Jihar Enugu, sakamakon kone mutane da ba a tantance adadinsu ba.
An kuma kone wata motar dakon kaya a yankin sakamakon tashe-tashen hankula.
- Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Sace Jarirai Sabbin Haihuwa A Anambra
- Shugaban Kasar Sin Ya Yi Shawarwari Da Manyan Shugabannin Kasar Saudiyya Da Kuma Gana Da Shugabannin Wasu Kasashen Larabawa Bi da Bi
A halin da ake ciki, rundunar ‘yansandan Jihar Enugu, ta tabbatar da aniyar ta na kamo wadanda suka kashe mutanen da har yanzu ba a tantance adadinsu ba a yankin a ranar Alhamis.
Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan jihar, Daniel Ndukwe, ya rabawa manema labarai, ta karyata rade-radin da ake yadawa cewa motar da aka kona a yayin harin na dauke da bindigogi da alburusai da kuma ‘yan bindiga.
Ndukwe ya ce kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Ahmed Ammani, tare da kwamandan runduna ta 82 na rundunar sojojin Nijeriya, Enugu, Birigediya Tuni da Janar M. K. Ibrahim da wasu manyan hafsoshin tsaro sun ziyarci inda harin ya faru domin tantance adadin barnar da aka yi.
“Kwamishanan, yayin da yake jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan aika-aikar da kuma wasu hare-haren da aka samu a yankin, ya bayyana karara cewa rundunar ‘yansanda tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro ba za su kasa a gwiwa ba. Ya ce ba za su saurara wa maharan da masu aikata wasu hare-hare da kisan kai a yankin ba.
“Ya kuma kara tabbatar wa al’ummar Eha-Amufu kan alkawarin da hukumomin tsaro suka dauka na daukar matakai don magance matsalar tsaro a yankin, tare da umarce su da su kasance masu bin doka da oda, su ba da hadin kai ga jami’an tsaro,” in ji shi.