Magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, sun yi barazanar cewa za su hada karfi da karfe su kare kawukansu muddin in jami’an ‘yansanda da sauran hukumomin tsaro ba za su iya karesu daga sake kai musu wani hari a nan gaba a jihar Ribas ba.
Idan za tuna, wasu da ake zargin ‘yan daba ne da yawansu ya haura 200 a ranar Alhamis sun kai harin gidan shugaban kwamitin yakin zaben dan takarar shugaban kasa na PDP, Sanata Lee Maeba a garin Fatakwal inda suka jikkata Yayansa da farfasa motoci har guda hudu.
Da ya ke ganawa da ‘yan jarida a garin Fatakwal jimkadan bayan kammala ganawa da ko’odinetocin kananan hukumomi na yakin zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, tsohon ministan Sufuri, Dakta Abiye Sekibo ya roki jami’an tsaro da su kara kaimi wajen sauke nauyin da ke kansu.
Sekibo, wanda shi ne daraktan yakin zaben a jihar, ya ce, aikin gwamnati ne kare rayuka da dukiyar jama’a.
Ya ce, a yayin zaman masu sun tattauna kan hare-haren da aka kai wa mambobinsu da kuma jikkata wasu da aka yi. Don haka ne ya ce dole ne su dauki matakan da suka dace wajen kare kawukansu daga wannan batun.
“Da farko dai mun gaya wa mutanenmu cewa su sanar jami’an tsaro duk wani abun da ke faruwa a kusa da su a kananan hukumomin su da zarar sun ga wani abun zargi.
“Muna kira ga hukumomin tsaro da su ke aikin da suka yi alkawarin yi. Su sauke nauyin da ke kansu kada su bari mu fara daukan matakan kare kanmu a wannan jihar.”