Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutum uku daga cikin mutum takwas da ake zargi da yin fyade da kashe dalibar Jami’ar Illorin mai shekara 24 a duniya, Olajide Blessing Omowumi, a ranar 2 ga watan Yuni, 2021.
Babbar kotun Jihar Kwara da ke zamanta a Ilorin ce ta yanke wannan hukuncin a ranar Talata.
- Gwamnatin Ebonyi Ta Ba Da Umarnin Kashe Duk Wanda Aka Gani Da Bindiga
- Kanu Ya Yi Tur Da Kai Hare-Haren ‘Yan Bindiga A Kudu Maso Gabas
Mutum uku da aka yanke wa hukuncin da wasu da ake zargi Gwamnatin Jihar Kwara ce ta gurfanar da su a gaban kotun cikin kara mai lamba KWS/33c/c/2021 dauke da tuhume-tuhume guda 11 da suka hada da fashi da makami, mallakar Malamai ba bisa ka’ida ba da kuma fyade hadi da sauran tuhume-tuhume.
A hukuncin da mai shari’a Ibrahim Adebayo Yusuf, ya yanke ya ce ya kama mutum ukun da laifin kisan kai da aikata fashi da makami.
Jagoran shigar da karar kuma tsohon kwamishinan shari’a na jihar Kwara, Barr. Salman Jawondo (SAN), wanda ya yi magana da ‘yan jarida bayan hukuncin ya yi karin haske da cewa bisa doka irin nau’in laifukan da wadanda ake zargi suka aikata hukuncin kisa ne ya dace da su bisa dogara da sashi na 221 na kundin laifuka.
“Wadanda ake zargi na hudu da na biyar an kamasu da laifin sace kudin mamaciyar a asusun ajiyarta. Bayan da suka kasheta, sun dauki na’urar cirar kudinta (ATM) da layukan wayarta. Sun canza lambobin sirri da hakan ya basu damar fitar da kudi har naira N149,000 daga asusun mamaciyar. An dauresu bisa laifin sata. An dauresu na tsawon shekara uku.”
“Sauran uku, wadanda ake tuhuma na shida, na bakwai da na takwas sun tsere
da wayo.”
Ya ce, idan aka duba shekarun wadanda suka aikata laifin da suke tsakanin shekara 19, 23 da saura abun takaici ne matuka.
Mutum takwas din da ake zargin su ne Abdulazeez Ismail, Ajala Moses Oluwatimileyin (da aka fi sani da Jacklord), Oyeyemi Timileyin Omogbolahan, Abdulkarim Shuaib (aka Easy), Kareem Oshioyemi Rasheed (Rashworld), Abdullateef Abdulrahman, Daud Bashir Adebayo (da aka fi sani da Bashman) da kuma Akande Taiye Oladoja.
LEADERSHIP ta labarto cewa rundunar ‘yansandan jihar Kwarai ta tabbatar da cewa an kashe Olajide ne a gidanta da ke Tanke a garin Illorin a ranar 2 ga watan June na 2021.