A ci gaba da yunkurinsa na sake fasalin ma’aikatar ma’adanai ta Jihar Osun, Gwamna Ademola Adeleke, ya bayar da umarnin dakatar da duk wasu kamfanonin hakar ma’adinai da ke gudanar da hakar ma’adanai na jihar nan take.
Sanarwar da kakakin Gwamnan jihar, Mallam Olawale Rasheed, ya raba wa manema labarai a Osogbo a ranar Laraba, ta ce dukkan masu gudanar da aiki za su kai rahoto ga kwamitin tantance kadarorinsu da Dakta B.T Salami ke jagoranta tare da kwafin takardar kulla yarjejeniya tsakaninsu da gwamnatin jihar.
- 2023: Matukar Mutum Ba Shi Da Katin Zabe Ba Zai Jefa Kuri’a Ba – INEC
- 2023: Matukar Mutum Ba Shi Da Katin Zabe Ba Zai Jefa Kuri’a Ba – INEC
Rasheed ya bayyana cewa, sanarwar da aka fitar daga sakataren gwamnatin jihar, Hon. Teslim Igbalaye, Gwamna Adeleke ya jaddada kudirinsa na kwato duk wasu kudade da Jihar Osun ke bi tare da dakatar da fasa kwaurin kadarorin jihar daga hako ma’adinai zuwa tara kudaden shiga.
“Dakatar da ma’aikatan za ta ci gaba da aiki har sai an kammala nazarin yarjejeniya tsakanin jihar nan da masu gudanar da ayyukan.
Sanarwar ta kara da cewa “Duk ma’aikatan su kai rahoto ga kwamitin ranar Litinin da karfe 12 na rana.”