Fitaccen malamin addinin musuluncin nan mazaunin Kaduna, Sheikh Dakta Ahmad Abubakar Gumi, a ranar Laraba, ya bayyana cewa katin zabe ya fi muhimmanci a yanzu fiye da takardar shaidar makaranta da fasfo na kasashen duniya, inda ya bukaci ‘yan Nijeriya da su karbi katin zabensu na dindindin (PVC) don su kada kuri’a a zaben 2023 don zabar shugabanni masu gaskiya.
Gumi, ya ce za a kirga kuri’u a zaben 2023, ya kuma bayyana cewa mallakar katin zabe ita ce kadai hanyar zaben shugabanni na gari a kauda azzaluma a kawo masu adalci.
Malamin, ya yi wannan kiran yayin da ya karbi nasa katin zaben, inda ya wallafa hakan ne a shafinsa na Facebook, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi amfani da ‘yancinsu ba tare da tsoratar da su ta hanyar tilastawa ko muzgunawa ba.