A watan Janairu na wannan shekarar aka samu rahoton garkuwa da mutane a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan. Hanyar ta kasance hanyar data fi daukar zirga-zirgar motoci a kasar nan, tana daukar mutane da kayyaki daga Arewaci zuwa Kudancin kasar nan.
A wani hari da ‘yan bindiga suka kai kwanan nan a daidai kauyen Abule Onigari inda suka kashe wani Direban motar haya, suka kuma yi awon gaba da fasinjoji 5. Kwana daya bayan nan kuma a daidai wurin da aka yina baya sai gashi ‘yan bindigan sun sake kai hari inda suka sace wata fittaciyar ‘yar fim mai suna, Bimpe Akintunde da ‘yarta. Tun daga wannan lokacin kuma sai rahottanin garkuwa da mutane a kan wannan babbar hanyar da ke da magtukar muhimmanci a zirga-zirgar mutane da kayyaki a tsakanin Arewaci da Kudancin Nijeriya ya cigaba da karuwa.
Matafiya da dama ciki har da Tsohon Mataimakin Shugaban Jami’ar Ibadan Farfesa Adigun Agbaje da wasu dalibai sun shiga hannun masu garkuwa da mutane a ranar 28 ga watan Oktoba, an sako ne bayan da aka biya wasu makudan kudade. Bayani ya nuna cewa, yawancin masu garkuwa da mutane na shigar sojoji ne yayin gudanar da ayyukansu.
Rahoton ‘yansanda ya nuna cewa, an kai harin ne a kusa da Jami’ar Dominion da ke a bangare na karshen babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, ‘yansanda sun bayyana yadda suka kai daukin gaggawa a karkashin jagorancin babban jami’in ‘yansanda na yankin, DPO da ‘yansanda Mobayil da gungun mafarauta suka kai daukin ceto mutanen a inda daya daga cikin ‘yansandan ya rasa ransa wasu kuma suka ji munanan raunuka, suna asibiti a halin yanzu suna karbar magani.
Yawaitar faruwar wannan ya fara zama wani kalubale ga mahukunta a halin yanzu. Haka kuma bayani ya nuna cewa, ‘yanbindigar na sanye ne da cikakkun kayan sojoji a yayin da suka datse hanyar. Abin lura a nan shi ne ayyukan wadannan ‘yan ta’addar ba su bar kowa ba a kan hanyoyin namu. In har wannan hare-haren suka ci gaba za su haifar da asarar rayuka da dukiyoyin al’umma masu dinbin yawa.
Amma ba wai a kan hanyoyinmu ne kadai ake fuskantar wannan barazanar ba. Kwanakin baya a cikin watan Yuni, an yi garkuwa da jami’a 10 na rundunar ‘yansandan Jihar Nasarawa a kan hanyarsu ta dawowa daga aikin sa ido a zaben gwamnan jihar Osun har zuwa wannan lokacin babu wani duriyar su. Bayani ya nuna cewa, an sace ‘yansandan ne a garin Obajana na Jihar Kogi a ranar 17 ga watan Yuli 2022, a daidai wurin da tireloli ke farkin da ake kira da ‘PTI Obajana’.
A daidai wannan lokacin na shekara da zirga-zirgar abin hawa ke kara karuwa, lokacin ne kuma da harkokin ‘yan ta’adda ke kaiwa makura. Kuma abubuwan kenan da ke faruwa a manyan hanyoyinmu a fadin tarayyar kasar nan.
Tuni ‘yan Nijeriya suka fara mantawa da kirga yawan garkuwa da mutanen da ake yi a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna dama hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna. Kasar bata kai ga farfadowa daga garkuwan da aka yi wa fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ba, inda wadanda aka yi garkuwa da su suka yi fiye da watannin 8 a hannun ‘yan bindiga.
Ana zargin an biya ‘yan bindigan Billiyoyin Naira a mastayin kudin fansa kafin a kai ga sako kashi na karshe na mutanen kwanan nan. A yau babu wani magana a kan gudanar da cikakken bincike ballatana a kai ga hukunta wadanda suka aikata wannan laifin. Maimakon abin ya ragu sai gashi ya koma wasu manyan hanyoyin wasu bangarorin kasar nan.
An ruwaito cewa, Babban Sufeton ‘Yansanda, Usman Baba ya ba jammi’ansa umarnin kasancewa a kan manyan hanyoyinmu musamman babbar hanyar Legas zuwa Ibadan don dakile karuwar ayyukan ‘yan ta’addan.
Bayanin jami’in yada labarai na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya nuna cewa, Babban Sufeton ya neni a sake fasalin ayyukan jami’an tsaron da ke aiki a manyan hanyoyinmu ta hanyar kai issasun jami’ai da kayan aiki don kare rayuka da dukiyoyin al’umma a wannan lokacin.
Ya kamata a ‘yansanda su dauki matakin da suka kamata na kare rayukan ‘yan Nijeriya wadanda babban laifinsu shi ne kasancewa a kan hanyoyin Nijeriya suna zirga-zirgar neman halaliyarsu. Bai kamata tafiya a kan hanyoyimmu ta zama mai hadari ba in har jammi’an tsaron da ke kan manyan hyanyoyimu suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. ‘Yan Nijeriya da dama na fuskantar zabin dukiyarsu ko kuma rayuwarsu, wannan na faruwa ne ba kawai don ayyukan ‘yan bindiga ba kawai harma da yadda jami’an tsaron suka yi watsi da ayyukansu na kare aukuwar ayyukan ‘yanta’adda.
‘Yanuwan wadanda aka yi garkuwa da su kan kai ga sayar da kaddarorinsu masu muhimmanci don biyan kudaden fansa don ceto ‘yanuwan nasu daga hannun ‘yan bindiga.
Manyan hayoyinmu na da matukar muhimmanci ba kawai a bangaren tattalin arziki ba kawai har ma don dorewar harkar siyasar kasar nan, a kan haka ya zama dole gwamnati ta dauki harkar tsaron rayuwa da dukiyoyinmu da matukar muhimmanci.