Da yammacin yau Asabar za a yi jana’izar tsohon shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Farfesa Abdullahi Mahdi wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar Juma’a.
Shahararren masanin tarihin kuma kwararre a fannin ilimi, ya rasu ranar Juma’a yana da shekaru 77.
- Samar Wa Sarakuna Hurumi A Tsarin Mulki Zai Kyautata Ci Gaban Kasa –Sarkin Misau
- Yadda Mai Juna Biyu Ta Rasa Ranta Wurin Ceton Mijinta Daga Hannun Masu Garkuwa
Mahdi ya yi aiki a matsayin shugaban Jami’ar Jihar Gombe da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Gombe.
Ya fara aikin koyarwa a shekarar 1984 a matsayin babban malami a fannin tarihi a ABU, sannan ya mataimakin shugaban Jami’a a tsakanin 1998 zuwa 2004.
Bayan gagarumar hidimar da ya yi wa kasa, marigayin malamin ya samu lambar yabo ta kasa ta CON.
Za a yi jana’izar ne da misalin karfe 4 na yammacin ranar Asabar a Jihar Gombe a fadar Sarkin Gombe.
Ya rubuta littafin ‘History of Nigeria for Schools and Colleges’ da sauran littafai.