Wasu manyan kwamandojin Boko Haram hudu sun mika wuya ga dakarun soji a Jihar Borno.
Kwamandojin, Mala’ana (Khaid), wanda ake kira Gwamna, Abu Dauda (Munzir), Modu Yalee (Kwamanda) da Bin Diska (Nakif), sun ajiye makamansu a ranar 12 ga Disamba, 2022 ga sojojin Operation Hadin Kai a karamar hukumar Gwoza da ke jihar.
- Sin Ta Gudanar Da Taron Shekara-Shekara Na Ayyukan Tattalin Arziki Don Tsara Shirin Shekarar 2023
- Za A Yi Jana’izar Tsohon Shugaban Jami’ar ABU, Farfesa Abdullahi Mahdi Da Yammacin Ranar Asabar
Lamarin dai kamar yadda wata majiya ta sirri ta tabbatar da Zagazola Makama, wani kwararre a fannin yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi, ya bayyana cewa maharan sun fito ne daga dajin Sambisa inda suke fakewa tare da kaddamar da yakin ta’addanci a jihar.
Majiyar ta ce su tsoffin kwamandojin Abubakar Shekau ne a sansanin Njimiya amma sun ajiye makamansu suka koma kungiyar ISWAP a tafkin Chadi bayan farmakin da suka kai dajin Sambisa a watan Mayun 2021, wanda ya yi sanadin mutuwar Shekau.
Sai dai daga baya kwamandojin hudu sun yi tir da ISWAP, inda suka gudu zuwa Sambisa inda suka kafa tanti suka koma aikin kansu.
Sun mika wuya ne saboda fargabar kawar da su a fagen saboda ci gaba da kai hare-hare kan maboyar ‘yan ta’adda da kuma hare-haren ‘yan hamayya.