Rahotanni sun ce a kalla mutane 12 sun rasa ransu bayan da wasu manyan motoci biyu makare da waken suya da kantu suka yi taho mu gama a hanyar Lambata zuwa Agaie zuwa Bida.
BBC ta rawaito ce wa, Shugaban hukumar kiyaye afkuwar hadura a jihar Neja, Kumar Tsukwam, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce hadarin ya afku ne a ranar Asabar da misalin karfe biyar na safe.
- Ambaliyar Ruwa: Ministar Jinkai Ta Kaddamar Da Rabon Tallafi Ga Mutum 5,428 A Neja
- Yadda Mutuwar Abokai Biyu Ta Fallasa Lalacewar Asibitocin Jihar Neja
Ya ce bayan afkuwar hadarin ta ke mutum 12 suka rasa ransu, yayin da wasu 10 kuma suka samu raunuka kuma tuni aka kai su zuwa asibitin Agaie don duba lafiyarsu.
Tsukwam, ya ce manyan motocin da suka yi hadarin na dauke da mutane 75 wadanda suka nufi jihar Legas daga arewa.
Ya kuma danganta afkuwar irin wadannan hadurra da gudun wuce kima da kuma rashin kiyaye dokokin hanya.
Daga nan ya ba wa masu ababan hawa shawara a kan su rinka takaita gudu da kuma kula da kiyaye ka’aidojin tuki da hanya.