Akalla wasu mutum takwas ne aka gurfanar da su a gaban kotun majistare da ke zamanta a Ibadan kar zargi cire sassan jikin wani mutum.
Wadanda ake tuhumar, wadanda ba a bayar da adireshinsu ba, an rufe su ne bisa zargin yanke sassan jikin wani mutum da ya mutu.
- NDLEA Ta Kwace Miyagun Kwayoyi Na Biliyan 450 A Wata 22 – Buba Marwa
- Banda Akwai Doka Da Mun Shiga Gidan Gwamnatin Bauchi Mun Kwato Mulkinmu —Adamu
An kuma tuhume su da laifin hada baki da kuma rashin mutunta gawar.
Dan sanda mai shigar da kara, Mista Philip Amusan, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a ranar 13 ga watan Disamba a unguwar Gbedun da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Ya yi zargin cewa wadanda ake tuhumar sun yi wa gawar wani marigayi Nimotalahi Amidu kutse ta hanyar datse kanta da wasu sassan jikinsa.
Amusan, ya ce laifin ya ci karo da sashe na 517 da 242(1) na dokokin laifuka na Jihar Oyo, na shekarar 2000.
Sai dai wadanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin.
Alkalin kotun, Misis O. A Akande, ta bayar da belinsu a kan kudi Naira 50,000 kowannensu da kuma gabatar da mutumin daya da zai tsaya musu.
Ta dage sauraron karar har zuwa ranar 22 ga Fabrairu, 2023, domin sauraren karar.