• English
  • Business News
Sunday, July 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsare-tsare Na Zahiri Da Za Su Matso Da Mutane Kusa Da Gwamnati

by Dokta Nasir Aminu
3 years ago
in Rahotonni
0
Tsare-tsare Na Zahiri Da Za Su Matso Da Mutane Kusa Da Gwamnati
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Sa-in-sa da ake yi tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi kan wanda zai yarda ya dauki nauyin karuwar talauci a tsakanin mutane ba shi ne abun dubawa ba.

Dukkanninsu suna neman wanda za a zarga ne a tsakaninsu a maimakon su duba mafita amma sun ki. Gwamnonin jihohin da suke gardama sun hadu a mataki daya, maimakon wani ya fara tunanin tsare-tsaren da za su kawar da talaucin da ke damun mutane.

  • Banda Akwai Doka Da Mun Shiga Gidan Gwamnatin Bauchi Mun Kwato Mulkinmu —Adamu
  • Shehu Sani Ya Yaba Wa ‘Yansanda Kan Cafke Wadanda Suka Farmaki Tawagar Atiku A Borno

Tarihi ya nuna cewa gwamnoni za su iya taimakawa wajen rage talaucin kamar yadda muka sani. Misali Sanata Ahmed Makarfi wanda ya bi wasu tsare-tsaren jam’iyyarsa ya gabatar da wasu ayyuka a Jihar Kaduna wanda tsarin ya fara tun daga kasa. Wannan tsarin zai fi tasiri ga al’umma da suke can kasa.

A karkashin mulkin Ahmed Makarfi tsakanin shekara ta 1999 zuwa 2007, gwamnatin Jihar Kaduna ta kashe Naira biliyan 98 wajen gudanar da manyar ayyuka a ko’ina cikin jihar. A lokacin da aka daidaita tashin abubuwa a shekarar 2020 jimillan yake daidai da Naira biliyan 526. Wanda yake daidai da Naira biliyan 66 a duk shekara. Wannan kudi za a ga kamar sun yi kadan. Duk da haka jihar ta yi kokarin yin ayyuka kanana da matsaikaita da kuma manya-manya.

Ayyukan dai sun hada da gina hanyoyi a birane da kauyukan jihar, da manyan gine-gine da samar da kayayyakin noma da gina makarantu da asibitoci da gina wuraren koyon sana’o’i da samar da ruwan sha mai tsafta ta hanyar haka rijiyar burtsatsi a tsakanin al’umma da samar da kayayyaki a asibitoci da sanya wutar lantarki a kauyuka da kirkirar gundumomin raya kasa.

Labarai Masu Nasaba

Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu

Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki

Gwamnatin Jihar Kaduna ta samar da wani kwamiti da ya bayyana cewa gwamnatin ta gina hanyoyi sama da 200 a fadin jihar. Wanda ya hada da hanyoyi a kauyuka da kuma birane wadanda suka hada garuruwa.

Don abubuwan ci gaba su daidai a tsakanin al’umma, an samar da yankunan ci gaba guda 46 a karkashin ma’aikatan kula da ci gaban kauyuka da al’umma. An sami wutar lantarki da yawa a kauyuka karkashin mulkin Ahmed Makarfi wanda ya tabbatar da cewa gaba dayan jihar an hada su da babban layin wutar lantarki na kasa. Gwamnatin ta gina gidajen ‘yan majalisa da gyara kwatas-kwatas na gwamnati sama da 700 tare da gine-gine gwamnati a jihar. Haka kuma mafi yawansu a yanzu an sayar da su. Ayyukan ya bai wa mutanen karkara damar samun karuwar tattalin arzikinsu wanda ya rage talauci.

A ayyukan da aka yi a birni, akwai tsohuwar gadar saman nan ta Kawo wanda ya zama na farko a Arewa don babu jihar da ta fara yin irinsa a wancan lokaci. Kuma za a iya cewa wannan aiki ne ya zama hasashe har wannan gwamnatin ta fadada shi. Gwamnatin ta kammala aikin Gamji Gate da kuma fadada Murtala Skuare da bangare na biyu na gidan gwamnati mai suna General Hassan Usman Katsina wanda ya zama na zamani.

Gwamnatin kai-tsaye tana shirin kawar da talauci ne a cikin al’umma, kamar samar da kananan basuka ga kungiyoyi da kuma daidaikun mutane. Abubuwan da aka amfana sun hada da tsabar kudi da ababen hawa da gidaje da sauran abubuwan gudanar da kasuwanci. Kananan basukan ya taimaka matuka wajen fitar da daruruwan mutane daga cikin talauci.

A bangaren lafiya kuwa, gwamnatin ta gina sabuwar kwalejin kimiyyar lafiya da kwalejin horas da masu jinya da unguwar zoma. An gina ne tare da kara darajar manyan asibito da cibiyoyin lafiya a jihar gaba daya su koma na zamani. Gwamnati ta ci gaba da samar da kayayyakin gwajin HIB da magunguna da kuma gina cibiyoyin kula da lafiyar hakora da wuraren bayar da jini a dukkanin jihar.

Idan kuwa aka koma bangaren noma, gwamnatin ta kirkiro da shirin nan na a koma gona ga mutum 2,300 da tare da shirye-shirye na musamman a kan aikin noma. Kayayyakin noma da suka hada da takin zamani sun yi sauki kuma ana samunsu a ko’ina a jihar, yayin da gwamnati ta bayar da tallafi na musamman a kan farashi mai rahusa. Ta sayi taraktoci sababbi sama da 250 tare da hadin gwiwar kananan hukumomin jihar da samar da magungunan kwari da iri na zamani da kuma kayan feshin maganin. An sha yashe madatsun ruwa a jihar domin samun isasshen ruwa da kuma taimaka wa wajen noman rani. Jihar ba ta fuskanci matsala a kan noma ba da ya kai ga karancin abinci fiye da yadda ake ciki a yanzu.

A bangaren ilimi kuwa, gwamnatin ta zuba jari sosai don ci gaban mutane. Daya daga cikin aikin da ta yi da har yanzu ake cin moriyarsa a bangaren cibiyoyin ilimi na gaba da sakandare su ne, kamar jami’ar Jihar Kaduna da ke cikin garin Kaduna wanda a lokacin da aka samar da jami’ar kudin makaranta yana da sauki ga talakawa. A shekarar 2022 jami’ar ta yaye dalibai sama da 10,000. Ana bayar da tallafin karatu ga ‘yan jihar wanda yake matsakaici shi ne a bai wa dalibai 12,500, amma a shekarar 2004/2005 an bai wa sama da mutum 20,000 tallafin karatu.

Haka kuma gwamnatin ta samar da wuraren koyar da sana’o’i ga mata a dukkanin kananan hukumomi 23 da suke jihar.  A banagren ilimi na bai-daya, an sami azuzuwa 1,800 da ofisoshi da bayuka da magudanan ruwa a jihar duka an gina su a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2005. Haka kuma an gyara azuzuwa sama da 4,500 da ofisoshi tare da sanya kujeru wanda har yanzu ana amfani da su.

Wadannan ayyukan ci gaba ya sanya gwamnati da ta biyo baya ba ta da wasu ayyuka a wuyanta da yawan gaske. Kuma wadannan nasarori sun sanya mutane sun matso kusa da gwamnati. Sai suka rika ji su ma suna cikin bangaren gwamnati ana tafiya tare da su, an rage talauci an inganta ilimi da habaka lafiya da samar da gidaje da sauran abubuwan more rayuwa.

Lallai kuwa al’umma sukan ji dadi idan suka an sami ci gaba.  Sakamakon abun da aka samu an kara abubuwan bukatuwa kamar lafiya da ilimi da kuma inganta rayuwa. Labarin nasarar da aka samu ba za a manta da shi ba. Jihohi kamar su Bauchi da Katsina har yanzu suna duba ayyukan da tsofaffin gwamnoninsu suka yi masu, Ahmed Mu’azu da Ummaru Ya’adua wadanda suka yi mulki a tsakanin shekara ta 1999 zuwa 2007.

A yanzu sakamakon da yake nunawa babu kyau, wanda yake nufin tsarin da ake yi ba ya aiki. Wasu suna nuna cewa komi daidai ne, amma kuma suna tunanin samun wani sakamako daban. A shekara 2023, dole ne mu canza tsarin ta hanyar zaben wadanda suka cancanta, idan ba haka ba, za mu ci gaba da zama a yanayin da muke ciki. Allah ya kyauta.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: BuharigwamnatiTsare-Tsare
ShareTweetSendShare
Previous Post

Gwamna Gombe Ya Taya Kiristoci Murnar Kirsimeti, Ya Hore Su Kan Zaman Lafiya

Next Post

In Gwamnati Ta Yi Mana Dam A Hunkuyi  Za Mu Wadata Nijeriya Da Dankalin Turawa -Umaru Dikko

Related

Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu
Rahotonni

Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu

1 day ago
Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki
Rahotonni

Rayuwar Aso Rock: Shugabannin Nijeriya 4 Da Suka Mutu Bayan Kammala Wa’adin Mulki

2 days ago
Fyade
Rahotonni

Nijeriya Na Kashe Naira Miliyan 4.3 A Kullum Don Ciyar Da Wadanda Ke Jiran Hukuncin Kisa

1 week ago
APC
Manyan Labarai

2027: Gangamin ‘Yan Adawa Ya Sa APC Fafutukar Neman Mafita

1 week ago
Majalisar Dokokin Nijeriya Ta Sanar Da Dakatar Da Ayyukanta Saboda Alhinin Rasuwar Buhari
Labarai

Na Shiga Aikin Soja Domin Gujewa Yin Auren Fari Da Ƙuruciya — Buhari

2 weeks ago
Ko Yanzu Tinubu Ya Yi Rawar Gani, Kuma Yana Ƙoƙari Sosai – Buhari
Rahotonni

Muhimman Abubuwa 10 Da Kowa Zai So Ya Sani Game Da Marigayi Shugaban Ƙasa Buhari

2 weeks ago
Next Post
In Gwamnati Ta Yi Mana Dam A Hunkuyi  Za Mu Wadata Nijeriya Da Dankalin Turawa -Umaru Dikko

In Gwamnati Ta Yi Mana Dam A Hunkuyi  Za Mu Wadata Nijeriya Da Dankalin Turawa -Umaru Dikko

LABARAI MASU NASABA

Gwamnan Bauchi Ya Sulhunta Rikicin Manoma Da Makiyaya A Darazo

Gwamnan Bauchi Ya Sulhunta Rikicin Manoma Da Makiyaya A Darazo

July 27, 2025
Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana

Sin Ta Samu Ci Gaban Aikin Jigilar Kaya A Rabin Farko Na Bana

July 27, 2025
Kudin Shigar Da Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Samu A Lokacin Zafi Na Bana Ya Zarce Yuan Biliyan 5

Kudin Shigar Da Kasuwar Fina-Finai Ta Sin Ta Samu A Lokacin Zafi Na Bana Ya Zarce Yuan Biliyan 5

July 27, 2025
Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu

Shanghai Ya Gabatar Da Shirin Gina Yankin Motoci Masu Tuka Kansu

July 27, 2025
Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani

Sin: Fasahar Rage Asarar Hatsi Ta Yi Amfani

July 27, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Wasu Sojojin Bogi 2 A Legas

‘Yansanda Sun Kashe ‘Yanbindiga Uku Da Kama AK-47 Guda Goma

July 27, 2025
Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa

Shetima Zai Wakilci Nijeriya A Taron Tsarin Abinci A Addis Ababa

July 27, 2025
Gwamnati Ta Ba Da Wa’adin Mako 6 Don Kammala Ginin Rukunin Gidaje A Kano

Gwamnati Ta Ba Da Wa’adin Mako 6 Don Kammala Ginin Rukunin Gidaje A Kano

July 27, 2025
Super Falcons Za Su Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu

Super Falcons Za Su Samu Kyakkyawar Tarɓa Daga Gare Ni A Abuja — Tinubu

July 27, 2025
ADC Ce Za Ta Haɗa Kan Arewa Wajen Kawo Ci Gaba — Mark

ADC Ce Za Ta Haɗa Kan Arewa Wajen Kawo Ci Gaba — Mark

July 27, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.