Har kullum shaidun gani da ido na kara tabbatar da aniyar kasar Sin ta gina alummar duniya mai makomar bai daya ga kowa, kuma tana ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, da aiwatar da sauye-sauye masu inganci a gida, da gudanar da hadin gwiwa domin cin gajiyar juna tsakaninta da sauran kasashe, da aiwatar da manufofin bunkasar duniya baki daya.
Ko da a ’yan kwanakin baya bayan nan ma, sai dai jakadan Sin a Amurka Qin Gang ya kara nanata wadannan manufofi na kasar Sin, cikin wani sharhi da aka wallafa. Kuma hakan na zuwa ne a gabar da Sin din ke kara fuskantar suka daga wasu kasashen yammacin duniya, wadanda ke kallon kasar a matsayin barazana gare su, duk da ba sa iya gabatar da sahihan dalilai na tabbatar da zargin nasu.
Kafin hakan, yayin taron wakilan jamaa na jamiyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin karo na 20 wanda ya gabata a watan Oktoba, mahukuntan kasar sun jaddada manufofin waje na kasar, manufofin da suka kunshi wanzar da zaman lafiya, da ingiza ci gaban duniya baki daya, yayin da take fatan gina alummar duniya mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama.
Karkashin manufofin kara bude kofa ga waje, tuni kasar Sin ta kafa yankunan gwaji na cinikayya maras shinge har 21, tare da fadada yawan yarjejeniyoyin cinikayya cikin ’yanci daga 10 zuwa 19, ciki har da cikakkiyar yarjejeniyar hadin gwiwar raya tattalin arziki ta shiyya ko FTA, irinta mafi girma a duniya.
Yanzu haka karin kasashen duniya musamman masu tasowa, na cin gajiya daga babbar kasuwar kasar Sin, wanda hakan ya kara budewa kasashe masu tasowa kafofin shigar da hajojinsu zuwa kasuwannin Sin. Karkashin manufofinta na samar da gata ga kasashe masu tasowa, Sin ta dage harajin shigo da wasu hajoji daga wasu kasashe masu rauni, ta yadda za su kai ga bunkasa gajiyar da suke samu daga cudanya da kasar. A hannu guda Sin din ta cire karin wasu sassan zuba jari daga jerin sassan da a baya aka sanyawa shinge ga masu zuba jarin waje, daga sassan 93 a baya zuwa 31 a yanzu.
Bugu da kari, wasu alkaluma da bankin duniya ya fitar sun nuna yadda kasuwannin Sin ke kara fadada, da janyo hankulan masu zuba jari. Alkaluman sun nuna yadda kasar Sin ta daga zuwa matsayi na 31, cikin jerin kasashe masu saukin gudanar da hada-hadar cinikayya a duniya, wanda hakan ya nuna cewa, kasar ta samu karin maki 65 cikin shekaru 10 da suka gabata a wannan fanni.
Idan kuma aka tabo batun tallafin wanzar da zaman lafiya, mun san cewa kasar Sin na kan gaba a duniya, a jerin kasashen dake samar da taikamo ga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD, yayin da manufofinta na wanzar da ci gaba, da jure kalubalen da duniya ke ciki ta fukar raya tattalin arziki a gida, ke kara ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya.
Duk da bambance-bambance dake tsakanin Sin da kasashe daban daban ta fuskar tarihi, aladu, zamantakewa da salon jagoranci. Masharhanta na cewa, kasancewar bil adama na rayuwa a duniya daya, kamata ya yi alummun duniya baki daya su rungumi akidun kasar Sin na kawar da sabani, da nunawa juna yatsa, ko mayar da wasu kasashe saniyar ware, ta yadda dukkanin sassan duniya za su mutunta juna, da bunkasa zaman lafiya, da cin gajiya tare, domin a tafi tare a tsira tare. (Saminu Alhassan)