Sama da mutane 200 ne suka bace yahin5da kadarorin miliyoyin kudi suka kone kurmus sakamakon tashin gobara a yankin Elekahia a Jihar Ribas.
An rawaito cewar lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na safiyar ranar Juma’a, wanda ake zargin kalanzir ne ya haddasa tashin wutar.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun tafi hutun bikin karshen shekara, yayin da wasu kuma na wajen aiki lokacin da lamarin ya auku.
Jami’in hukumar kashe gobara ta jihar, John Nnemeka, ya ce sun isa wurin da lamarin ya faru da wuri amma sun gaza shiga sakamakon yanayin yadda gine-ginen gidajen suke.