Wannan ne karshen tattaunawar da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA ta yi da daya daga cikin manyan jarumai mata da suka fi fitowa a matsayin iyaye a masana’antar Kannywood, wadda muka kawo muku kashin farko a makon jiya. Ga ci gaban:
Jama’a na mamakin yadda wasu daga cikin Jarumai kannywood ke yin kudi da zarar sun shiga cikin masana’antar, sabanin sauran Jaruman da suka dade a cikin masana’antar ba tare da sun yi kudin ba, sai ma bukatar taimako da suke yi, shin akwai wani aiki da ake yi na musamman ne cikin masana’antar, ko wata sana’a wadda take saurin kawo kudaden ko makamancin haka?
Ana yawan yi mana wannan tambayar kwarai da gaske, ita dai harka ta rayuwa kowacce ba ta rasa sila. Kin ga dai ga mu a ciki shekara da shekaru muna ta yi, toh ita silar rayuwa ce za ki ga ‘da’ ka haife shi kai talaka ne dan ya zo ya zama me kudi, danka ne kai ka haife shi, bare harka da kowa dirowa yayi da kafafuwansa, kuma harkar fim ki rike wannan abun, abu guda uku ne dole wanda ya shigo harkar fim sai ya kasance da guda daya; Ko dai wata sha’awa ce ta kawo ka, wasu sha’awa ce take kawo su, sun ga ana yi su ma bari su shiga, wasu kuma akwai wata bukata da suke da ita ba su samu ba, sai su rabe da wannan harkar, dan su cimma biyan buwatarsu. Na uku kuma neman kudi ne, neman rufawa kai asiri, neman sutura, shi ne yake kawo su. Toh! duk abun ka in kana cikin masana’antar a cikin abu ukun nan sai ka tsinci kanka a daya. Saboda haka kin ga wadanda suna da wasu abubuwansu na yi sha’awace ta kawo su toh kin ga akwai abubuwansu da za su ba su kudinsu a can gefe. Wasu kuma wadanda akwai bukatar da ta kawo su, wata dama suke son su samu ta game da wannan fim din, suka dan rabu da shi toh kin ga suma suna da wani abu na su a gefe ba fim din zalla suka sa a gaba ba. Wasu kuma sadidan fim din suka zo dan su nemi rufin asirin, toh sanadin fim din sai kuma ya zame musu sila ta samun wani abu.
Ya za ki bambantawa masu karatu bambancin da ke tsakanin fina-finan baya dana yanzu, har ma da ita kanta masana’antar?
Gaskiya kam! akwai bambanci, bambanci na hauhawar abun duniya, yanzu kamar yadda nayi miki maganar shekara ashirin baya, da dubu dari ko saba’in sai ka yi fim gwaggwaba, kuma a sami alheri, wadanda daga can baya suka samu alheri a harkar fim, wasu ma yanzu ba ma harkar suke ba dan ba za su iya na yanzu ba. Yanzu irin kamfanin su Sarauniya sun ci ribar fim, amma da ya zama yadda ya zama din nan ko kafin rasuwar Aminun Sarauniya, daraktan na su, Allah ya rahmamasa, wallahi sun ja jiki suka ce ba za su iya ba. Saboda yanzu an samu matsalar tsadar abun duniya, yanzu idan ka ce za ka yi fim, kamar wannan ‘siries’ din, in dai managarci za a yi wallahi sai ya lamushe milyan biyu, a haka za ka tsakurota ta dawo ga aiki ya koma Youtube. Fim din na kasuwar ma yanzu ya gagara, da CD za a bubbuga akai kasuwa a siyar a samu alheri, toh yanzu ga abu yadda ya zama na zamani, ka kashe makudan kudi, sai kuma abin da ka gani. Kuma abin da zai baki mamaki tun a wancen lokacin na shigo harkar a lokacin ‘scene’ daya ana ba da dari biyar 500, wasu ma dari uku 300. Sarauniya su suka fara kai ‘scene’ ya zama dubu daya 1000, kuma da babu bambancin wannan karamin Jarumi ne, wannan babba ne. Ina fadar wannan ina kara fade, babu wannan bambancin, abin da babban Jarumi zai fi ka jan sina-sinai, in kai sin uku a ba ka dubu uku, in ya yi sin goma a ba shi dubu goma, bambancinku kenan. Amma yanzu sai a dunkule kudi a bawa babban Jarumi, kuma kai ba ka wuce dan rakiya ba sai abin da ka gani. Akwai bambanci sosai da za ka yi fim a kai kasuwa ka samu riba ninkin baninkin kudi a wadace, ma’aikata kowa a yi masa biya yadda ya kamata, amma yanzu abubuwa duk sun zama ga kudin za a kashe ba kananan kudi ba, amma wasu daga cikin ma’aikatan wallahi kuka suke, suna wayyo! Wayyo!!. kamar yadda kika ce kana yin fim din baka wuce a taimake ka ba. Ai bambanci ne, da yadda aka taso a can baya har yanzun hakan ake, wallahi dan fim ba zai tafi yawon neman taimako ba, an samu canje-canje ne. Bugu da kari ga rashin shugabanci, su kansu shuwagabannin ga su nan ga irinsu. Wata irin rayuwa ga ta nan ta kashin dankali, abu ya yi ta baka haushi kai ta samun bacin rai.
Yanzu kwanaki wasu abubuwa da suka taso na wani ‘Workshop’ da aka yi, aka ce za a yi ‘training’ har dan takarar shugaban kasar nan ya zo aka babbada kyaututtukan kudade, in Allah ya yarda masu ido da kwalli ne suka samu, wani sai dai wannan zancen ya ji, mu duk abin da ake an yi da mu, amma in Allah ya yarda labari ya sha bamban, ba mu isa a samu a wannan layin ba, amma sanda za a yi an ce mu zo an kira mu mun kuma je duk abin da za a yi an yi da mu. Amma kuma sauran bayanin sai ya sha bamban, saboda mu ba mu kai wannan matsayin ba. Harkar tana da wani irin mataki-mataki in ba ka kai ba, kai ba kowa ba ne, toh! da ba haka ba ne, kowa duk iri daya ne, abin da babban Jarumi zai fi ka, ya fi ka yawan sina-sinai. Kana aiki yana aiki, duk abin ku iri daya ne. Kuma matsayi dole daman ko a cikin gida ne, dole wani ya fi wani matsayi, dole wani zai dan dara wani, saboda shaharar wani za ta dan dara ta wani, fitar ka a fim za ta dara na wancen, toh dole a samu dan wannan darin, amma a cikin harkar duk kowa daya ne, yanzu abubuwan duk sun bambanta, an samu sabanin hakan.
Yanzu shi babban Jarumi wanda duniya ta san da zamansa ya shahara, idan yayi ‘scene’ guda kudinsa ya fi na Jarumin da bai shahara ba komai yawan ‘scene’ din da yayi kenan?
Akwai bambanci tsakanin babban Jarumi da kuma karami, akwai bambanci ba karami ba kuwa, ai shahara ma wani abu ne, ubangiji Allah ya sada mu da alkhairi, mun godewa Allah, da yadda muka tsinci kai da yadda kuma muka kasance a cikin al’amarin.
Me za ki ce game da irin kallon da al’umma ke yi wa ‘yan fim na ganin kamar gwamnati na tattare kudade tana ba su?
Wannan ai ba gwamnati ba ce take tattare kudi take bayarwa ba, wannan siyasa ce kawai, gwamnati tana yi ne saboda ita ma ta gyara kujerar ta, suna yi ne kawai dan ai musu kamfen idan ya wuce shikkenan. Ana tattara kudi ana bawa manyan Jarumai, saboda Kamfen, ana gamawa shikkenan magana ta wuce, kuma su ma manyan Jarumai ake bawa su ne masu yin Kamfen dan saboda su duniya ta sani.
Mene ne burinki na gaba game da harkar fim?
Babban burina yadda na fara aikin nan lafiya Alhamdulillah, fatana ubangiji Allah ya sa mu gama shi lafiya, salamun kaulun min rabbir rahimu.
Wacce shawara za ki bawa sauran abokan aikinki na masana’antar Kannywood game da wannan sana’ar taku ta fim, har ma da su kansu Furodusas din?
Shawarar da zan bayar ga fudusoshi shi ne; mu zama tsintsiya madaurinmu daya, idan aka hada kai toh al’amari zai ci gaba, a kuma rinka sa Allah a cikin lamari ana kamanta kiyaye hakkin jama’a, domin duk abin da za ka kiyaye hakkin wanda kake tare da shi toh! in sha Allah al’amarinka zai yi gaba yadda ya kamata, Ubangiji Allah ya dafa mana ya kuma hada kahunanmu, Allah ya dai-daita tsakani ya ba mu hadin kai, kuma ya ciyar da wannan masana’anta ta mu gaba alfarmar Annabi da Alkur’ani.
Wanne kira za ki yi ga masu kallo, da kuma masu kokarin shiga cikin masana’antar ta kannywood?
Masu kallo sai na ce su rinka yi mana fatan alkhairi da kyakkyawan zato, domin ba kowa ne gurbatacce ba. Masu kokarin shigowa harka ta wannan masana’anta tamu kuma, kiran da zan yi gare su shi ne; Idan Allah ya sa sun shigo to su dauki harkar fim sana’a ce wadda za ta rufa musu asiri, kuma idan an fara a kiyaye mutunci, idan ka rike mutuncinka in Allah ya yarda za ka yi komai lafiya ka gama lafiya. Duk wanda suke kokarin shigowa Allah ya dafa ya ba su sa’a da nasara, domin harka ce me fadi kuma kullum mutane kara shigowa suke yi, A kuma kiyaye dukkan wasu ka’idoji da kuma sharidodi da suke tattare da cikin masana’antar, toh! sai ka ga an yi lafiya an gama lafiya, Allah ya ba mu dacewa.
Ko akwai wani kira da za ki yi ga gwamnati game da wannan sana’a taku?
Kiran da zan yi ga Gwamnati shi ne; Muna so gwamnati ta ja masana’antar Kannywood a jiki, ta yadda za a rinka tallafawa harkar ta zama yadda ya kamata, ba wai dan fim yana dan matse-matsen ya zai yi ba, ba wai ace bukatarsu da mu lokacin siyasa in tayi a kira manyanmu a babbasu kudade, a tattara madaidaita da matsakaita, dana kasa a hadu ayi ta kide-kide da wake-wake da raye-raye, a rarrabawa mutane abin da Allah ya sa ya kama rabonsa ne, shikkenan kowa yayi nasa waje, shikkenan magana ta wuce sai dai kuma wani lokacin. Fatan mu gwamnati a ja wannan masana’anta a jika, yadda za ta ci gaba yadda dan fim shi ma zai zama wane ne, saboda duk duniyar fim da ake fim, ba a fim dan a ci abinci, fim ake dan a samu kudi, amma ba wani fim da yake da koma baya, yake da nakasu irin fim din Hausa. Saboda babu tallafi, ba ruwan gwamnati da harkar kannywood, kawai babban burinsu idan sha’ani ya tashi a gayyato su, masu waka da abubuwa su yi an wuce wajen, ubangiji Allah ya sa gwamnati ta ja wannan masana’anta a jika, yadda ‘ya’yanta za su ji dadi suma su tsaya akan kafafuwansu, ya zama dan fim in an nuna shi waccen dan fim din ne, fim din yake tsurar fim yake, kudin fim shi ne ya rike shi. Allah ya sa da rabo, fatanmu kenan, Allah ya sa gwamnatinmu ta fadaka, ta kuma gane ‘yan fim mutane ne da suke da bukatar tallafi, daga gwamnati, dan an ce a nuna maka yadda ake kama kifi, toh ya fi a kamo kifin a baka, domin in ka kasa ka cinye zuru za kai. Amma idan an nuna ma yadda za a kama kifin sai ka dulmiya ka kamo kayanka. Toh! in aka tsayawa mutane akan yadda za su tsaya akan kafafuwansu, ai ya fi a dinga basu wannan kudade a rarraba wasu su samu, wasu ba su samu ba, ayi ta maganganu ayi ta korafi, wasu ma su rinka dora Allah ya isah, Allah ya dafa mana ya ganar da gwamnatinmu.
Me za ki ce da wannan shafi na Rumbun Nishadi har ma da ita kanta Jaridar LEADERSHIP Hausa gaba daya?
Alhamdulillahi, Ma Sha Allah! Ba abin da za mu ce da wannan kamfani na Leadership sai ubangiji Allah ya daukakata. Ni ma’abociyar karatun wannan Jarida ce Leadership Hausa, ina tabbatar miki ina jin sai da na kai ina da Jaridar Leadership ta shekara goma. Toh! ba abin da zance da wannan Jarida sai dai na ce Allah ya daukakata, ya kara daukakata, ya kara muku kuma basira da fusahar zance wajen iya tambayoyi, gaba dai – gaba dai Jaridar Leadership Allah ya kara daukaka.
Ko kina da wadanda za ki gaisar?
Zan yi gaisuwa amma sabida yawan mutanen da zan gaisar, wajen yayi kadan na fade su, zan yi su a jimla a dunkule. A cikin masana’antar mu, ina gaishe da dukkanin furodusas dina, ina gaishe su, wadanda suke sakani a cikin aikinsu da wadanda ma ba su saka ni ba duk ina gaishe su. Daraktocinmu na Kannywood baki daya ina gaishe su, wanda nake aiki da su, da wadanda ma ban taba aiki da su ba duk ina gaishe su. ‘Yan uwana Jarumai abokanan aikina kaf! na wannan masana’anta tamu ina gaishe su baki daya, Allah ya kara hada kahunanmu ya kuma tabbatar mana da alkhairi. Ina gaishe da ‘yan uwana baki daya, masu kaunata kaf! ina gaishe su, wanda na sani da wadanda ban sani ba. Da ma’abota kallon fina-finai na wadanda muke rayuwa tare da su ina gaishe su, gaba daya.
Ina gaida ‘ya’yana, ina gaida ‘yan uwana na jini, wanda muke uwa daya uba daya, ina gaishe su. Ina gaida ‘yar autana Maryama Autar Mama ina gaisheta da kyau-da kyau, karatu da aka yi ubangiji Allah ya tabbatar da alkhairi, ya ba da dacewa, ya ba da nasara, Allah ya sa ya zamo sanadin da ita ma za ta tsaya akan kafarta, har wani ma ya huta ta karkashinta dan alfarmar sayyiduna rasulullahi (SAW). Ina gaida jikokina iyalan Baba gaba dayansu, nawa na cikina dana ‘yan uwana Allah ya albarkace su, suma ina gaggaishe su. Ke ma Rabi’at Sidi Bala wakiliyar Leadership Hausa da muka dade da ke muna wannan doguwar hira da ke ina gaishe ki sosai. Ma’aikatan Jaridar Leadership Hausa gaba daya rankatakaf! ina gaishe su baki daya shugaban Sashin Leadership Hausa Abdulrazak Yahuza Jere shi ma ina gaishe shi, Allah ya daukaka wannan kamfani na Jarida taku Leadership, Allah ya daukakata ya kai ta gaba gaba gaba gaba… In sha Allahu, ya zamo duniya ko ina an san da ita alfarmar Annabi da Alkur’ani.
Muna godiya kwarai da gaske, duk da cewa akwai sauran tambayoyin da mun so ki amsa mana su, sakamakon wajen ya yi kadan ya sa dole mu dakata anan, sai na ce mu tara wani lokacin da yardar Allah.
Ni ma na gode sosai Allah ya saka da Alkhairi ya kara muku ci gaba, Amin.