Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi Allah-wadai da harin da aka kai wa ayarin motocinsa, inda ya ce za a gurfanar da wadanda suka kai harin.
Tambuwal ya shaida wa manema labarai a wajen taron masu ruwa da tsaki da suka yi da masu rike da mukaman siyasa a jihar, cewa an kama wasu daga cikin maharan kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da su gaban kuliya.
- ‘Yansanda Sun Kubutar Da Sakataren Ma’aikatar Aiyuka Na Jihar Filato Daga Hannun Masu Garkuwa
- ‘Yan Bindiga Sun Sake Afkawa Garin Jere Sun Yi Awon Gaba Da Mutane
“Hukumomin tsaro na binciken lamarin. An dai kama wasu. Kuma an tabbatar da cewa doka za ta yi aiki,” in ji gwamnan.
Tambuwal ya ce: “Abin takaici ne jiya a hanyarmu ta dawowa daga Wammako, a ofishin Sanata Aliyu Magatakarda Wammako, wasu ‘yan iska sun kai hari kan ayarina a kan hanyarmu ta zuwa gidan gwamnati.
“Ba za mu lamunci duk wata al’ada ta tashin hankali a Jihar Sakkwato ba,” in ji gwamnan.
“Don haka ina kira ga daukacin shugabannin siyasa na Sakkwato da su guji tashin hankali; sannan kuma su shawarci dukkan mabiyansu da magoya bayansu da su fita yakin neman zabe cikin lumana; kuma kada a yi tashin hankali.
“Kamar yadda aka sani, mun yi imani da zaman lafiya. Muna kira da a zauna lafiya a Jihar Sakkwato, ba tare da la’akari da bambance-bambancen jam’iyyun siyasa, nasaba ko ra’ayi ba.”