Tsohon dan wasan Arsenal da Chelsea, Olivier Giroud yana daya daga cikin ‘yan wasan da kungiyar Manchester United ke son daukowa a watan Janairu.
Kungiyar na son daukar dan wasan dan kasar Faransa wanda ya taimakawa kasar kaiwa wasan karshe na cin kofin duniya na FIFA a shekarar 2022 a Qatar.
A watan Yuni ne kwantiragin dan wasan na AC Milan zai kare kuma har yanzu kungiyar ta Italiyar ba ta sake masa tayin tsawaita kwantiraginsa ba.
Dan wasan mai shekaru 36 ya shafe shekaru shida a Arsenal kafin ya koma kungiyar Chelsea inda ya zauna na tsawon shekaru uku.
A lokacin da yake Chelsea, Giroud ya lashe kofuna uku ciki har da kofin gasar zakarun Turai.
Ya zura kwallaye tara a wasanni 19 da ya buga wa AC Milan kawo yanzu.