Sama da mutane 500 cikin har da maza da matasa da kuma nakasassu sun karbi tallafin dogaro da kai a Jihar Jigawa da Gidauniyar Katar tare da hadin gwiwar Gidauniyar Malam Inuwa wacce shugaban hukumar bunkasa fasahar sadarwa (NITDA), Kashifu Inuwa ya kafa suka ba da tallafin.
Gabatar da tallafin ya gudana a ranar Litinin da ta gabata a shalkwatan gidauniyar da ke Hadejia cikin Jihar Jigawa.
Shugaban gidauniyar, Dakta Hussaini Baban ya bayyana cewa mata 200 an tallafa musu da kekunan dinki, sannan wasu mutum 300 sun sami tallafin injin malkade, sai kuma mutum 3 an ba su kwamfuta da mutum 13 da aka ba wa kayan aikin kafinta, haka kuma wasu 13 sun sami tallafin baburan hawa na guragu.
Gwamnan Jigawa wanda mataimakinsa Umar Namadi ya wakilta tare da Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Adamu Maje sun gode wa shugaban hukumar NITDA da gidauniyar ta kasar Katar.
Sauran manyan baki a wurin taron sun hada da shugabannin kananan hukumomi da ‘yan majalisa, inda daga karshe kuma suka ziyarci wuraren da za su sake aiwatar da ginin gidaje da makarantu bayan sun bude wanda suka yi.
“Rayuwar sadaukarwa irin ta Kashifu abin sha’awa ce ga kowa daga cikinmu, sirrin rayuwa shi ne bayarwa a lokacin da ake bukata, domin kaima idan ka ba wani, Allah zai ninka maka, don haka muna rokon ya ci gaba da bayarwa kar ya daina.
“Muna rokon Allah ya kara masa matsayi mafi daukaka, sannan ya yi maka kyakkywan karshe tare da gina maka gida a Aljannah,” in ji daya daga cikin mutanen yankin mai suna Tony ya bayyana.