An shafe shekaru 3 ana fama da annobar COVID-19 a duniya. Wannan ita ce annoba mafi tsanani da ta shafi lafiyar al’umma da aka fuskanta a tarihi, cikin shekaru 100 da suka shude.
Bisa alkaluman da hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar a baya-bayan nan, cikin shekaru 3 da suka gabata, adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a duniya ya zarce miliyan 660 a fadin duniya, kuma adadin wadanda suka mutu sanadiyyar cutar kai tsaye da wadanda ba na kai tsaye ba, ya kai gomman miliyoyi.
COVID-19 da ba a taba ganin irinta cikin shekaru 100 ba, ta fahimtar da mu cewa, hadin kai da goyon bayan juna su ne makamai mafi karfi da bil adama ke da su wajen yakar annoba.(Fa’iza Mustapha)