Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka saba yi a yau Talata cewa, a cikin shekarar da ta gabata, an ci gaba da raya shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” yadda ya kamata, ta yadda aka shigar da sabon kuzari ga farfadowar tattalin arzikin duniya.
Shekarar da muke ciki, shekara ce ta cika shekaru 10 da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da raya shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” cikin hadin gwiwa. Don haka za a ci gaba da aiwatar da manufar tattaunawa tare kan manyan manufofin hadin kai, da kafa dandalin hadin kai tare, da kuma more nasarorin da aka cimma kan hadin kan, tare da hada hannu da dukkan bangarori don neman ci gaba tare, da nufin kara habaka wadatar da wannan shawara, dake amfanar duniya da bil’adama ke samarwa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp