Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci masu kada kuri’a a Jihar Yobe da kuma yankin Arewa Maso Gabashin kasar nan da su tabbatar da cewa sun zabi Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa.
Da yake jawabi a taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a filin wasa na Damaturu, babban birnin Jihar Yobe, shugaban kasar a wata sanarwa ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya ce zaben Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima, ne kadai mafitar ‘yan Nijeriya.
- Birtaniya Na Son Taimaka Wa Nijeriya Ta Farfado – Atiku
- Aikin Hajjin 2023: Nijeriya Ta Kulla Yarjejeniyar Fahimtar Juna Da Gwamnatin Saudiyya
Ya ce idan ana bukatar tabbatar da dorewar ci gaban da aka samu a fannin tsaro, tattalin arziki da ilimi a kasar nan dole a zabi dan takarar na APC.
Shugaban ya sha alwashin cewa bayan nasarar da aka samu a kan ‘yan ta’adda a yankin, gwamnatin APC ta yi kokarin karya lagon duk wanda ke barazana ga hadin kan Nijeriya.
Shugaban da yake jaddada bukatar ilimi wajen yakar akidar ta’addanci ta Boko Haram, ya shaida wa iyaye a Yobe cewa: “Ku tabbata kun tura ‘ya’yanku makaranta ku fahimtar da su cewa duk abin da kuke da shi a duniya za a iya kwace muku, ilimi ne kadai ba za a iya kwace muku ba.
‘‘Ni maraya ne; ban san mahaifina ba. Na yi shekara tara a makarantar kwana kuma saboda ilimi aka kai ni aikin sojin Nijeriya.”
Ga masu rike da tutar jam’iyyar APC a zabe mai zuwa, shugaba Buhari ya kalubalanci su da su tabbatar da shugabanci na gari idan aka zabe su, ka da su bai wa jama’a kunya.
Ya bayyana cewa jam’iyyar mai mulki ta yi iya bakin kokarinta a cikin shekaru takwas da suka gabata a matakin tarayya kuma za ta ci gaba da tabbatar da ci gaba, wadata da kwanciyar hankali a Nijeriya.
A nasa jawabin, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da karairayi da jam’iyyun adawa ke yi wa gwamnatin Buhari.
“Wannan gwamnati gwamnati ce ta ci gaba, rikon amana da gaskiya,” in ji shi.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, wanda ya yaba wa Buhari kan samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan, ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta mayar da yankin cibiyar sarrafa kayan gona ta Nijeriya.