Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, Boko Haram ba komai ba ce illa damfara da aka shirya domin tarwatsa Nijeriya.
Shugaban ya bayyana haka ne a yayin da ya karbi bakuncin Kungiyar Manyan Limaman Kiristoci na Katolika da ke Nijeriya (CBCN) a fadarsa da ke Abuja, inda ya kara da cewa, an samu ci gaba sosai kan sha’anin tsaron kasar nan.
“Ban jima na da dawowa daga Jihohin Adamawa da Yobe. Lokacin da nake ziyarar can, na ji abubuwan da mutane suke fada, haka nan jami’an gwamnati. Dukkansu sun ce an samu ci gab ana yanayin da ake ciki daga 2015, musamman a Jihar Borno.
“Boko Haram ba komai ba ce illa damfara da munakisa da aka shirya don tarwatsa Nijeriya. Babu ta yadda za a yi ka hana mutane neman ilimi, al’umma tana bukatar ta samu ci gaba ta bangaren ilimi da kaifin basira,” in ji shi.
A halin da ake ciki kuma, Shugaba Buhari ya ce kungiyoyin ‘yan ta’adda ba za su sake yin wani katabus da sunan tasiri ba, saboda yadda gwamnatinsa ta yi musu raga-raga, inda kuma ya bukaci ‘Yan Nijeriya su ci gaba da bai wa jami’an tsaro cikakken goyon baya da hadin kai tare da bin doka da oda.
Ya bayyana hakan a lokacin da ya ziyarci Fadar Sarkin Damaturu a Jihar Yobe, Mai Martaba Hashimi El-Kanemi II, a ziyarar aikin bude wasu manyan ayyukan da gwamnatinsa tare da na Jihar Yobe suka aiwatar. Ya kara da bayyana cewa, gwamnati za ta ci gaba da kare ‘yancin kowane dan Nijeriya wajen samun ilimi, musamman ‘yan gudun hijira wadanda rikicin Boko Haram ta gayyara.
”Wanda zan iya cewa wata hudu masu zuwa, zan bar ofis, kuma zan ci gaba da abubuwan da suka kamata, sannan kuma ina da burin zan koma gefe in yi ritaya cikin aminci.
”Dole mu gina kyakkyawar fata a zukatanmu game da kasarmu, saboda abu ne mai muhimmanci mu tabbatar cewa bangaren tsaro da tattalin arziki suna kan gaba a kan komai.
”Haka kuma abubuwa da daman gaske sun faru a matsayinta na kasa, wanda nake kara kira gareku ku ci gaba da juriya tare da tsayin-daka, domin ba zamu bari wani ya sake hargutsa mu ba,” in ji shi.
Dangane da yadda aka samu ci gaba a sha’anin tsaron Arewa Maso Gabas, shugaban Nijeriya ya yaba wa Gwamna Mai Mala Buni da takwaransa na Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, bisa aiki tukuru wajen sake farfado da makarantu, asibitoci hadi da muhimman wuraren da ‘yan ta’adda suka lalata a jihohin.
Shugaba Buhari ya ce, ”Saboda akwai yunkurin da suka yi wajen ruguza Nijeriya baki daya, amma Allah bai yarda ba. Kuma cikin ikon Allah ga Nijeriya nan ta sake komawa yadda take a baya.”
Har wala yau, Buhari ya yaba da namijin kokarin sojojin Nijeriya tare da hadin gwiwa ‘yansanda bisa sadaukarwar da suka nuna wajen kare mutuncin Nijeriya.
Bugu da kari, Buhari ya nanata cewa a matsayinsa na wanda ya yi gwagwarmayar hadin kan Nijeriya a lokacin yakin basasa, babu yadda za a yi ga wanda ya tsinci kansa a wancan yanayin a ce zai amince wani mutum ya sake raba kan ‘yan kasa ba.”
A nashi bangaren, Gwamnan Jihar Yobe, Buni ya shaida wa shugaban kasa cewa, sakamakon kamarin rikicin Boko Haram, ita ma Fadar Sarkin Damaturu ba ta tsira daga mamayar ‘yan ta’addan ba.
”Haka zalika kuma, yau gashi zaman lafiya ya samu a kowane bangaren Jihar Yobe, babu wani yanki a jihar da yake a hannun mayakan Boko Haram.
”Wanda kafin hakan, a baya da za ka ajiye dala biliyan daya a wannan Fadar ka ce wani ya zo ya dauka, babu mutumin da zai yi kasadar zuwa kusa da ita. Amma bayan kasancewarka shugaban kasa, abin ya zama tarihi wanda al’ummar Jihar Yobe ke more ‘yancin zaman lafiya da suka samu.”
A nashi jawabin, Sarkin Damaturu ya bayyana godiyarsa ga shugaban kasa bisa inganta harkar tsaro a Nijeriya.
Ya ce, ”Saboda ko shakka babu mu a nan Jihar Yobe ganau ne dangane da kokarin da gwamnatinka ta yi na kawo ci gaba a kasa.”
Bayan ziyarar Fadar Sarkin Damaturu, tawagar Shugaba Buhari ta zarce wajen bude ayyukan da gwamnatin Jihar Yobe ta aiwatar da kuma wasu ayyuka wadanda ma’aikatar ‘yansanda ta aiwatar a jihar.
Ayyukan da suka hada da bude shalkwatar rundunar ‘yansanda, asibitin ‘yansanda tare da hanyoyi da makarantar sakandire ta ‘yansanda, wadanda aka kammala aikinsu a karkashin Safeto Janar, Usman Alkali Baba.
Har ila yau kuma, shugaban kasa ya bude filin jirgin sama (Muhammadu Buhari International Cargo Airport), kasuwar zamani a Damaturu, asibitin kula da lafiyar mata da yara a asibitin koyarwa ta Jami’ar Jihar Yobe, kana da bude rukunin gidaje 2600 wadanda jihar ta gina tare da makarantar Mega a rukunin gidaje na New Bra-Bra, wanda Gwamna Buni ya gina.