A makon jiya LEADERSHIP Hausa ta ruwaito cewa masarautar Bauchi ta tsige Alhaji Muhammadu Bello Kirfi daga sarautar Wazirin Bauchi bisa zarginsa da rashin da’a da biyayya ga gwamnan Jihar Bala Muhammad.
Sai dai wakilinmu ya binciko cewa rashin fahimta ce ta siyasa ta gitta a tsakaninsu. Ko da yake shi Bello Kirfi da gwamnan jihar dukkaninsu ‘ya’yan jam’iyyar PDP ne.
Rahotonni sun bayyana cewa, shi dai Bello Kirfi wanda dattijo ne kuma tsohon ministan ayyukan musamman a Nijeriya, kana dan gani kashenin Atiku Abubakar ne, ya kira wani taro inda ya bukaci jama’an Jihar Bauchi da su zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar amma a matakin gwamnan jihar kuma kowa ya zabi wanda yake so.
Ana ganin wannan dalilin ne ya fusata gwamna Bala Muhammad da har aka kai ga daukan matakin cire shi daga mukaminsa.
LEADERSHIP Hausa ta zanta da wani makusancin tsohon Wazirin Bauchi, Lawan Mukhtari Ladan, inda ya bayyana cewar babu komai a cikin lamarin illa batun da ya shafi harkokin siyasa da rashin fahimta irin ta siyasa.
“Wannan ba shi ne na farko da aka fara ba kuma dukkanin wadannan abubuwan da ka ga su na faruwa suna faruwa ne a kan gaskiya. Shi Alhaji Bello Kirfi mutum ne da yake da gaskiya yake da kaifi guda daya a dukkanin al’amuransa.
“Matsalar da ya samu a can baya aka dakatar da shi duka a kan irin wadannan abubuwan ne, zai zo ya fadi gaskiya ga gwamnati domin a samu gyare-gyare amma sai a zo ana samun matsaloli. Shi gwamna da ke jin giyar mulki sai ya yi abun da yake so.
“Yanzu dakatar da Baba Waziri da ya yi bai isa ya ce zai cire sunansa a zukatan jama’an Jihar Bauchi ba. Sannan kuma abun da ya faru shi ne, a matsayinsa na uban kasa ya ba da shawara cewa Bala Muhammad ya hakura da maganar takarar shugaban kasa tun da farko amma bai yi hakan ba tun daga lokacin ne fa aka fara samun matsala.
“Alhaji Muhammad Bello ya kira taro ya ce ga Allah ya kawo Atiku zai yi takarar shugaban kasa, yankinmu na Arewa Maso Gabas ba mu taba yin shugaban kasa ba amma yanzu ga dama ta samu don haka yana neman alfarman jama’a da su zabi Atiku.”
A nasa bangaren, kwamishinan kananan hukumomi da masarautun gargajiya na Jihar Bauchi, Honorabul Abdulrazak Nuhu Zaki, ya ce sarakuna ne suka dauki matakin ladabtarwa.
“Sun kawo min takarda na ainihin sallamar Alhaji Muhammadu Bello Kirfi daga matsayin Wazirin Bauchi a wannan lokacin wanda tuni aka maye gurbi sa da Garkuwan Bauchi, Alhaji Mohammadu Uba Ahmed Kari da aka daukaka matsayinsa zuwa Wazirin Bauchi.
“Da an taba koranshi, Mai girma gwamnan Jihar Bauchi ya yi kokari ya maida shi ba tare da masarautar Bauchi tana so ba, ya je ya samu Mai Martaba Sarkin Bauchi ya ce ya yi hakuri da duk abun da ya musu a matsayin babansa, amma bai fasa abubuwan da yake yi ba.
“Wannan ne ya shi Mai girma gwamnan ya ce shi ma ya cire hannunsa kamar yadda suka niyyar cire shi, kuma daga yanzu ba ruwansa domin abun da yake musu ba daidai ba ne.”
“In ma ya zama yaya ne dai an cire shi, muna wa wanda ya samu kujerar fatan Allah ya taimakeshi ya rike sarautar da mutunci.
Domin kujera ce wacce take da bukatar mutum ya kame ya zama yana kiyayewa daga shiga harkar da ba irin ta su ba,” in ji Zaki.
Kakakin Jam’iyyar PDP, Alhaji Yayanuwa Zainari ya karyata duk wata zance da ke cewa akwai baraka tsakanin Atiku da Bala, inda yake cewa dukkaninsu suna karkashin lema daya kuma kowa na taimakon kowa a cikinsu.
Ya ce, “Ai ba abun da zai hada mai girma gwamnan jihar Bauchi da Atiku, Allah ya yi su a jam’iyya daya kuma kowa zai taimaki kowa, sannan duk inda muka je da gwamna neman alfarmar kuri’a sai mun fara nema wa Atiku a matsayinsa na dan takarar shugaban kasa, to ka ga ba wata matsala.
“Ita maganar sarauta in ka duba ma shi Waziri ba mai zaban sarki ba ne, babu hannun gwamna a kan takardar Waziri domin sarki ne yake nada Waziri. Don haka ka da a hada maganar sarauta da maganar siyasa.”
Sai dai kuma a gefe guda, Bello Kirfi ya maka gwamnatin Jihar Bauchi a kotu bisa abun da ya kira cire shi ba bisa ka’ida ba.
A wata sanarwar da mai magana da yawunsa, Barista Yakubu Bello Kirfi ya fitar ya bayyana cewa an yada wani labari na karya da aka ce Muhammad Bello Kirfi ya sha alwashin sai ya yi duk mai yiyuwa domin dakile zarcewar Bala Muhammad.
“Hankulanmu sun karkata kan wasu rahotonnin da aka wallafa a ranar 8 da 9 ga watan Janairun 2023 da aka nakalto cewa Alhaji Dakta Muhammad Bello Kirfi CON, na cewa zai yi duk mai yiyuwa domin cire gwamna Bala Muhammad daga kujerar gwamna ta hanyar hana masa nasarar zarcewa a zaben 2023 da ke tafe.
“Labarin sam babu gaskiya a ciki. A matsayinsa na musulmi, yayi imani da kaddara, kuma Allah ne mai iko, yana kuma ba da mulki ne ga wanda ya so ya karba daga hannun wanda ya so a lokacin da ya so.
“Cire shi da aka yi a matsayin Wazirin Bauchi kuma mambar majalisar sarkin Bauchi da aka yi a ranar 3 ga watan Janairu, gwamnatin Bauchi ce ke da hannu a ciki inda ta yi amfani da masarauta kuma hakan ya janyo ce-ce-ku-ce sosai a fadin jihar.”
Tunin dai Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu ya nada sabon Wazirin Bauchi, Alhaji Mohammadu Uba Ahmad Kari.
Nadin na Kari na zuwa ne bayan tunbuke rawanin tsohon Wazirin Alhaji Muhammadu Bello Kirfi bisa abun da aka ce rashin biyayya da mutunta gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad.