Wasu ‘Yan bindiga dadi sun kai hari ofishin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ke karamar hukumar Enugu a jihar Enugu.
Harin wanda ya faru da karfe 9.12 na daren ranar Lahadi da ya janyo mutuwar jami’in hukumar ‘yansandan Nijeriya yayin da wani guda kuma ya gamu da raunuka yanzu haka yake amsar kulawar Likitoci a halin yanzu.
- Jami’an Tsaro Sun Kuɓutar Da Wata Soja Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Iyakar Enugu Da Imo
- An Kone Mutane Marasa Adadi A Wani Rikici A EnuguÂ
A wata sanarwar da INEC ta fitar tare da aiko da kwafinta ga LEADERSHIP a Abuja ranar Litinin dauke da sanya hannun Shugaban kwamitin yada labarai, Festus Okoye, ya ce, ‘yan bindigan sun yi fata-fata da kofar da jami’an tsaro ke gadi a ofishin.
Kan hakan, Okoye ya ce, maharan sun kasa shiga can cikin ofishin sakamakon tirjiya da suka fuskanta daga Jami’an tsaron ‘yansandan da na soja na bataliya 82 da suke Enugu.
“Cikin gaggawa bayan faruwar lamarin kwamishinan ‘yansandan jihar da kwamishinan zabe REC sun ziyarci wajen da abun ya faru. Jami’an ‘yansanda biyu da aka tura domin kare muhallin, daya ya mutu daya kuma ya gamu da raunuka amma yana amsar kulawar Likitoci a halin yanzu.
“Hukumar mu tana addu’ar Allah bai wa iyalan mamacin hakurin jure wannan babban rashin tare da addu’ar Allah bai wa wanda ya jikkata lafiya cikin hanzar.”
Okoye ya ce, kwamishinan zabe a jihar Enugu, Dr. Chukwuemeka Chukwu ya sanar da Shalkwatar hukumar kan harin da ‘yan bindigan suka kai Ofishin.
Sanarwar ta ce, tunin aka kaddamar da bincike kan lamarin domin cafko maharan.
Ya kuma ce za a sake gini get din jami’an tsaron da ‘yan bindigan suka lalata, ya kuma ce hukumar ta ci gaba da gudanar da shirye-shiryenta kan zaben 2023 da ke gabanta a jihar ta Enugu.